Ministan ya kara da cewa Ma’aikatar Bunkasa Masana’antar Karafa za ta bayar da tallafin manufofi da ababen more rayuwa, ciki har da hada ayyukan sufuri na Stellar Steel a cikin Tsarin Kasa na Ababen More Rayuwa, da kuma ba da dama ga rangwamen haraji da sauran abubuwan tallafi.
Sanarwar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen: “Kirkirar tsarin samar da karfe daga karfen kasa a cikin gida don rage dogaro da shigo da kaya da kuma ceton fiye da Dala biliyan 1 na kudin waje a kowace shekara.”
A nasa bangaren, Shuaibu ya jaddada cewa wannan hadin gwiwa na tsare-tsare zai bude sabon babi ga masana’antar karfe ta Nijeriya, tare da nuna jajircewar gwamnati wajen samun ci gaban masana’antu mai dorewa da sauya tsarin tattalin arziki.
A cikin jawabinsa, shugaban tawagar, Mista Li, ya tabbatar wa ministan cewa Stellar Steel Company Limited zai girmama dukkan yarjejeniyoyin da aka cimma, kuma za ta tabbatar da kammala aikin cikin lokaci, tare da kiyaye duk ka’idojin tsaro yadda ya kamata.
A yayin rattaba hannu kan yarjejeniyar, wakilan bangarorin biyu sun jaddada cewa hadin gwiwar zai ta karfafa masana’antun kasar, ya kara damar ayyukan yi, kuma ya inganta canja wurin fasaha a wannan fanni.














