Gwamnatin Chadi ta sanar da rufe iyakarta da Nijeriya nan take, tana mai cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda dalilan tsaro, bayan rahotannin da ke cewa Amurka na shirin kai harin Soji a yankin Yammacin Afrika. Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar damuwa a yankin Sahel.
Majiyoyin Soji a N’Djamena sun tabbatar a ranar Litinin cewa Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya bayar da umarnin kulle iyakar ƙasar gaba ɗaya da Nijeriya, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga arewacin Nijeriya na shirin tserewa zuwa cikin Chadi. An ce umarnin ya shafi manyan hanyoyin shiga da fita, musamman ta yankin tafkin Chadi.
- Gwamnoni Sun Yi Kira Ga Tinubu Kan Ci Gaba Da Hako Mai A Kolmani Da Tafkin Chadi
 - Za A Iya Samun Biliyoyin Daloli A Noman Zogale Da Kantu A Tekun Chadi
 
Rahotanni sun ce an sanya rundunar Sojin Chadi cikin shirin ko-ta-ƙwana, tare da tura dakaru da motocin yaƙi zuwa muhimman hanyoyin da ke haɗa ƙasashen biyu. Wannan mataki, in ji majiyoyi, yana nufin hana shige da fice ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare yankunan kan iyaka daga barazanar ta’addanci.
A cikin wata sanarwa, Shugaba Déby ya ce gwamnati ba za ta yarda wata ƙungiya mai ɗauke da makamai ko wata ƙasa ta waje ta yi amfani da ƙasarsa wajen cimma wani buri ba. Ya ce, “Ba za mu bari wata ƙungiya ko wata ƙasa ta waje ta karya dokokinmu ko ta yi amfani da ƙasarmu don aikata wani abu da zai bar illa ga yankin ba.”
Masu lura da harkokin tsaro sun ce wannan mataki na iya yin tasiri ga hulɗar kasuwanci da zirga-zirga tsakanin kasashen biyu, musamman ga ƴan kasuwa da matafiya daga Borno, da Yobe da N’Djamena, inda ake yawan safarar kaya da abinci tsakanin ƙasashen.
			




							








