Bisa lamarin da ya ya shafi lamuran kasa da kasa, musamman idan aka samu wata matsala da ta shafi huddar jakandanci, a kan yi kokari ne, domin lalubo da mafita.
Amma, irin daukar irin wannan matakin, batun bahaka ya ke ga shugaban Amurka ba, duba da yadda Donald Trump ba, duba da yadda a ranar Asabar da ta gabata, ya yi kurarin barazanar aukawa Nijeriya da yaki da makamai.
- Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
- Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
Trump, ya yi wannan barazanar ce kan cewar, ana yiwa mabiya addiin Kirista kisan gilla a kasar nan, wanda hakan ya sanya, ya umarci sahsne yaki na Amurka, wato Pentagon, da ya fara shirya makamai, domin kawo wa Nijeriya yaki, wanda a na sa ganin ikirarin na sa na kisan gillar, tauye hakkin ‘yan Adama ne.
Kazalika, Trump ya alakanta kasar, a matsayin cikin jeren kasa ta musamman da bata bayar da ‘yancin gudanar da yin addini, wanda kuma alhali, ba shi da wasu kwararan hujjoji kan wannan ikirarin na sa.
Wannan batun, na barazanar Trump, ta samo asali ne ga furucin matsalar tsaro a kasar nan, da wani sanata na majalisar Amurka Ted Cruz, ya jiero da ita.
Sai dai, bisa batun gasakiya, karya ce tsagwaronta kan batun kisan kiyashin da ake yamadidin cewa, ana yiwa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya.
Bugu da kari, wannan batun ana wani yunkuri ne na son kawo rudadi a kasar nna, musamman duba da cewa, masu son kawo rudadin, a zahiri, sun jahilci irin yanayin sarkakiyar lamarin tsaro na kasar nan.
Wannan Jaridar, ta sha yin tsokaci, kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar kasar nan, tare da kuma yawan gabatar da kira ga Gwamnatin kasar da ta tashi tsaye, domin daukar matakan da suka dace, na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.
Batun aikata ta’addanci, yin garkuwa da mutane da kuma aukuwar rikici a tsakanin manoma da makiyaya, matsaloli ne, da ke shafar kowannen dan Nijeriya, wanda kuma Trump da masu ba shi shawara, suka jahilci hakan, musammman duba da cewa, akasarin wadannan matsalalin, na aukuwa Musulmi da Kirista ne.
Wani abin duba wa a nan shi ne, akasarin hare-haren ‘yan ta’addara Boko Hrama na kai wa kan Musulmi da ke Arewacin Nijeriya, wanda Trump, ya kafa hujar da cewa, ana kashe Kiristoci ne, inda kuma hare-haren, suka nuna cewa, anfi hallaka Musulmai, fiye da Kiristoci.
Ayyana matsalar tsaron kasar da Trump ya yin a yi wa Kiristoci kisan kare dangi wani abu ne, da yake da matukar hadari.
Martanin da shugaba Bola Tinubu ya mayarwa da Trump kan wannan ikirarin na sa, abu ne da ya dace, musamman cewar da ya yi a Nijeriya ana bai wa kowanne dan kasar, ‘yancin yin addininsa, ba tare da wata tsangwama ba, musamman kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar, ya tanadar.
Bugu da kari, idan har Trump na nuna damuwa kan ikirarinsa na ana yi wa Kiristocin kasar kisan gilla, to su kuma Kiristocin da aka hallak a zirin Gaza biyo bayan hare-haren kasar Isra’ila fa?
Kuma mai ya sa ba zai yi amfani da karfin ikon gwamnatinsa na dakatar da yakar kasar Ukraine, da kasar Rasha ke ci gaba da yi ba, duba da yadda aka kashe dubban Kiristoci a kasar?
Amsar a nan ita ce, Trump ba wai na da nufi bai wa Kiristocin kasar nan kariya bane, wani bakar manufa ce kawai da yake son cimma burinsa.
Tarihi ba zai sanya mu yi saurin manta wa da mamayar da Amurka ta yiwa kasar Afghanistan a 2001 ba don kifar da gwamnatin Taliban wadda ta alakantan, a matsayin ‘yan ta’adda.
A lokacin mamayar, sama da mutane 200,000 ne, suka rasa rayukansu, amma duk da hakan, Taliban ta sake dawo wadda a yanzu, ta ke ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar.
Kazalika, Amurka ta mamaye kasar Iraki a 2003, ta cere shugaban sojin kasar kasa marigayi Saddam Hussein, inda sama da mutane 150,000 suka rasa rayukansu sabo da hare-haren Amurka.
Hakazalika, ta kai wata mamayar a kasar Lbiyia ta cere marigayi Gaddafi, wanda har yanzu, kasar ba ta saitu ba, inda kuma burbushin yakin na Lbiya ya haifar da shigar makamai cikin kasar nan da ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga daji da kuma wasu Fulani ke yin amfani da su, wajen kai hare-hare a Nijeriya.
Yin amfani da karin soji da Amurka ta yi barazanar yi kan Nijeriya ba sanya matsalar tsaron kasar nan, ta kau ba, sai dai ma, kara tabarbarar da tsaron kasar.
Idan har da gaske Amurka ta ke yi na taimaka wa Nijeriya ta magance kalubalen rashin tsaronta ba ta hanyar barazana ya kamata ta bullowa kasar ba, kamata ya yi ta taimaka wa Nijeriya da kudade da makamai domin kawo karshen matsalar da kuma yin musayar bayanan sirri.
Amma yi wa Nijeriya wannan barazar, tamkar wani cin fuska ne.
A zahiri barazanar ta Trump, ba wai yana nufin bai wa Kiristocin Nijeriya kariya bane, amma wani salon na ne kawai na son nuna karfin iko da kuma son kawo rabuwar kanuwanan ‘yan Nijeriya.
Ya kamata Trump ya mayar da hankali kan matsalolin da ke ci gaba da addabar kasarsa ne, ba wai yin shiga sharo ba shanu, kan batun da ya shafi Nijeriya ba.
Sai dai, a nan za mu iya cewa, wannan barazar ta sa, dole ne ta zama wata ankawarar ga masu rike da madafun iko a kasar nan, wajen lalubo da mafita kan matsalar tsaro da kasar da kasar ke ci gaba da fuskanta.













