Majalisar Wakila ta nuna ƙin amincewa da kakkausar murya kan harin da wasu ƴan bindiga suka kai wa tawagar ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Borgu/Agwara ta jihar Neja, Hon. Jafaru Mohammed Ali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro da dama tare da jikkatar wasu.
Majalisar ta bayyana harin a matsayin mummunan aika-aikar ta’addanci da rashin imani, tana mai nuna alhini kan rayukan da suka salwanta tare da alƙawarin tallafawa duk wani yunkuri na kama masu laifin don su fuskanci hukunci.
- Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi
- Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu
Harin ya faru ne a ranar Talata da rana a kan hanyar Lumma–Babanna da ke ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja, wacce ta shahara da matsalar hare-haren ƴan fashi da kuma ƙungiyoyin ɓa ɓarayi masu ɗauke da makamai daga iyakar ƙasashen dake makwabtaka da Nijeriya. Rahotanni sun ce harin ya auku tsakanin ƙarfe 1:00 da 2:00 na rana, a yayin da tawagar ta isa garin Babanna, kusa da iyakar Jamhuriyar Benin.
Wannan sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya fitar a ranar Juma’a ya tabbatar da cewa an kashe jami’an tsaro da dama, wasu kuma sun ji rauni, kuma motocin sun lalace.
Majalisar ta bayyana cewa Hon. Ali na kan aikin mazaɓarsa lokacin da iftila’in ya faru, tana mai jaddada cewa irin waɗannan al’amura na nuna yadda ƴan majalisa ke shiga wurare masu haɗari don tabbatar da aiyuka ga jama’arsu.
“Wannan mummunan hari ya yi sanadiyyar mutuwar jaruman jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen kare shi,” in ji sanarwar.
Majalisar ta yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu, da hukumomin tsaro, da al’ummar jihar Neja, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙin cikin gaggawa.
A ƙarshe, Majalisar Wakilai ta sake tabbatar da jajircewarta wajen ganin an tabbatar da tsaron jama’a da jami’an gwamnati. Ta yi alƙawarin ci gaba da bai wa ɓangaren zartarwa da hukumomin tsaro goyon bayan doka wajen yaƙi da ta’addanci, da fashi da makami, da sauran nau’o’in laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasar.














