Gwamnatin Tarayya ta nemi ƴan Nijeriya da su ƙwantar da hankali duk da tutsun diflomasiyya da ya taso tsakanin Nijeriya da Amurka.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a Dutse, Jihar Jigawa, yayin ziyarar gaisuwa ga Gwamna Umar A. Namadi.
- Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari
- Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da dukkan abin da ya kamata wajen tabbatar da tsaron Nijeriya daga duk wata barazana da zata kawo ruɗani, da kuma gyara duk wani tarnaki a dangantakar mu da abokan hulɗarmu na ƙasa da ƙasa, don haka, ƴan Nijeriya su samu nutsuwa,” in ji Idris.
Ministan ya ziyarci jihar Jigawa ne domin halartar taron matasa na Arewa maso yamma na shekarar 2025 da kuma Gabatar da Nasarorin Shugaba Tinubu bayan shekaru biyu a ofis.














