Wani kwararre a fannin kiwon kajin gidan gona, Dakta James Baba Wageti, ya bayyana cewa; akasarin wadanda suke kiwon kajin gidan gona, don samun riba, na tabka kuskure a matakan farko na gudanar da kiwon; wanda hakan ya sa ba sa iya samun riba mai yawa.
James, wanda ke da kwarewa a fannin ta kusan kimanin shekara 31, ya zayyano kura-kuran da wasu masu kiwon ke yi.
- Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla
- Akwai Bukatar Karfafa Hadaka Domin Ciyar Da Tashoshin Jiragen Ruwa Gaba A Afirka —Dantsoho
Kazalika, ya kuma bayar da shawarar da ta kamata su bi, wajen kaucewa yin kura-kuran, mussaman a lokacin da ya fi dacewa, su sauya kajinsu na gidan gona da ke shirin fara yin kwai.
Ya bayyana cewa, a bisa ka’ida, kamata ya yi masu kiwon su sauya masu waje, ko kuma sanya su a cikin keji daga tsakanin mako13 zuwa 15.
Ya kara da cewa, yin amfani da wannan tsarin, na taimaka wa kajin na saba wa da wuri da kuma kara samun kwai mai tarin yawa.
Ya ci gaba da cewa, rashin bin ka’idar; na iya jawo masu yin asara tare kuma da shafar lafiyar kajin.
Har ila yau, ya yi nuni da cewa; nau’in kajin gidan gona, kamar na ‘Isa Brown’, akasari suna kai wa girman daga kashi 75 zuwa kashi 95 ba su kammala girmansu ne, wanda a lokacin nauyinsu ya kai zuwa mako 12.
“A daidai mako na 16, lokaci ne kajin ke samun sauyin da zai ba su damar fara yin kwan tare kuma da samun karfin jikinsu,” in ji kwararren.
Lokacin Da Ya Kamata A Sauyawa Kajin Wajen Da Za Su Yi Kwai:
Kwararen ya bayar da shawara kan lokacin da ya dace a sauyawa kajin wajen da za su fara yin kwan, wanda ya sanar da cewa; ya kamata hakan ya kasance a tsakanin mako hudu ko akalla mako biyu, kafin su fara yin kwan.
Ya ce, ‘yar wannan tazarar da ake samu, za ta bai wa kajin damar sabawa da sabon wurin kwannan da aka sauya musu da tsarin cin abincinsu da kuma rage musu wahalar da suka fuskanta a yayin kwashe su zuwa sabon wajen tare kuma da kare su daga rage nauyin jikinsu.
“A bisa kwarewar da nake da ita a fannin har ta tsawon shekara 31, kajin gidan gonar da aka sauyawa waje, nauyinsu na raguwa zuwa kashi 10 a cikin 100 ko sama da haka, wanda hakan ke taimaka musu murnurewa kafin su fara yin kwan,” a cewarsa.
Matsalolin Da Ke Afkuwa Na Sauya Musu Bayan Mako Na 16:
Sauya musu waje a cikin mako na 16 ko ga haka, zai iya lalata inda kajin ke ajiye da kwansu tare kuma da shafar karfin jikinsu. Kazalika, ya kara da cewa; hakan zai kuma iya yi wa kwanduwar kwan illa da kuma shafar kwanciyar kwanduwar kwan.
Shawara Ga Masu Kiwon Kajin Gidan Gona:
Kwararren ya sanar da cewa, ya kamata masu kiwon su tabbatar sun sanya su a keji ko kuma sun sauya musu wajen a tsakanin 13 zuwa 15 yadda jikinsu zai kasance a daidai kashi 85, bayan sauya musu wajen.
Ya kara da cewa, su kuma tabbatar da cewa; nauyinsu ya kai kilo 1.35 a yayin da suke mako na 16 ko kuma nauyinsu ya kai kilo 1.5 a yayin da suke mako na 18.
A cewarsa, ana kuma bukatar su samar musu daidaito na abinci mai gina jiki da kuma sanya ido kan yanayin haske a lokacin da za a sauya musu wajen.
Mako na 18 Zuwa Na 43 Su Ne Lokuta Mafi Tsanani: Dakta Wageti ya alakanta mako na 18 zuwa na 42 a matsayin lokacin da ya kamata mai kiwon Kajin gidan gona ya tabbatar yana sanya ido matuka duba da cewa; lokuta ne da suka kasance mafi tsanani da ke nuna lokacin fara yin kwan kajin gidan gona.
Ya ce, a tsakanin wannan lokacin ne, makin da nauyin kajin ke karuwa daga kilo1.5 zuwa kimanin daya zuwa kilo 2.0, kuma lokaci ne da suke shirin fara yin kwai tare kuma da karuwar girman kwansu zuwa akalla daga kilo 40 zuwa kilo 60.














