Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ya tafi zuwa jihar Neja domin jagorantar ƙoƙarin ceto ɗalibai fiye da 200 da ’yan bindiga suka sace a makarantar St. Mary da ke garin Papiri. Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana haka a shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa, inda ya ce wannan mataki na cikin hanzarin gwamnati na ganin an kubutar da dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su.
Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta tabbatar da cewa mutane 227 ne aka sace, ciki har da ɗalibai 215 da malamai 12. Shugaban CAN a Neja, Rev. Bulus Dauwa Yohanna, ya ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici, yayin da maharan suka shiga makarantar da tsakar daren Alhamis, suka harbe maigadi sannan suka yi awon gaba da ɗaliban firamare da sakandaren makarantar.
- Muna Bukatar Gudunmawar Addu’o’in ‘Yan Nijeriya Don Yaki Da Matsalar Tsaro — Badaru
- Badaru Na Da Kwarewar Jagorantar Ma’aikatar Tsaro – ANA
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta riga ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun yankin saboda barazanar tsaro, amma makarantar St. Mary ta buɗe ba tare da izini ko sanarwa ga hukumomi ba. Wannan ya faru ne kasa da sati guda bayan sace dalibai mata 25 a makarantar sakandaren ’yanmata da ke Maga, jihar Kebbi.
A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta ce ta baza jami’an tsaro domin ceto dukkan ɗaliban da aka sace a Neja da Kebbi. Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya ce kamar yadda aka tura shi Kebbi, haka ma Babban Ministan Tsaro Muhammad Badaru zai isa Neja don sa ido kai tsaye kan aikin kubutarwa da tabbatar da komawar daliban zuwa iyalansu lafiya.














