Majalisar Dattijai a ranar Talata ta nuna sabuwar damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da ya gajiya.
‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi.
- Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
- Matar Sarkin Suleja Mai Martaba Malam Muhammad Awwal Ibrahim Ta Rasu
Wadannan kuduri sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi gargadi cewa tsaro ya kai matakin tashin hankali wanda ke bukatar gaggawa da matakin kasa mai karfi.
A yayin tattaunawa, Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi Central) ya bayyana yanayin a matsayin “barazana mai tsanani ga rayuwar kasa”, yana rokon abokan aikinsa da su tabbatar da abin domin magance matsalar.
Tinubu Ya Shaida Wa Duke na Edinburgh Cewa Gyare-gyarenmu Zai Karfafa Matasa Nijeriya
“Ba za mu siyasantar da wannan lamari ba domin wadannan yara ba namu bane,” in ji shi.
Sanata Aminu Tambuwal (PDP, Sokoto South) ya ce kasar ta fada cikin tarkon abokan gaba, yana gargadin cewa gazawar haduwa don yaki da rashin tsaro zai iya barazana ga makomar Nijeriya.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan (APC, Yobe North), ya nuna damuwa cewa duk da manyan kasafin kudi da aka ware ga bangaren tsaro, hare-hare da kisan kai na ci gaba da faruwa.
“Wadannan yara ne shugabannin gobe. Dole mu yi duk mai yiwuwa domin kare su,” in ji shi.
Sanata Orji Uzor Kalu (APC, Abia North) ya zargi gwamnonin jihohi da watsi da rawar da kundin tsarin mulki ya basu a harkar tsaro.
“Tsaro ba nauyin gwamnatin tarayya kadai bane. Dole ne a shigar da gwamnonin jihohi,” in ji shi, yana kara da cewa a lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan Abia, ya kaddamar da wannan kalubale.
Sanata Bictor Umeh (LP, Anambra Central) ya yi kira ga amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan leken asiri domin gano da ceto yaran da aka sace, yayin da Sanata Simon Lalong (APC, Plateau South) ya tambayi dalilin da ya sa ’yanmatan makaranta ke ci gaba da zama makasudin hare-hare.
“In an ce yarinyar ta aikata laifi a ina? Shin muna cewa ba ma son ’yanmata su je makaranta? Wannan gaggawa ce ta kasa baki daya,” in ji shi.
Majalisar Dattijai ta amince da karin tayin da Sanata Adams Oshiomhole (APC, Edo North) ya gabatar, wanda ke nema a dauki matasa 100,000 cikin rundunar sojoji.
Oshiomhole ya jaddada cewa sabbin dauka dole ne a horar da su sosai kuma a ba su kayan aiki domin tunkarar ’yan bindiga, ’yan ta’adda, da sauran kungiyoyin tashin hankali da ke harzuka da kasa.
Majalisar Dattijai ta kuma goyi bayan kara amfani da fasahar leken asiri da na’ura mai hangen nesa na zamani domin yakar rashin tsaro da taimakawa wajen gano ‘yanmatan makaranta da aka sace a Jihar Kebbi.













