A yau Asabar ne aka bude taron kungiyar G20 a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, taron da a karon farko yake gudana a nahiyar Afirka, bisa taken “Hadin kai, daidaito da dorewa”.
Taron na kwanaki biyu, a wannan karo ya shaida muhimmin lokaci ga nahiyar Afirka, na neman daga matsayinta a jagorancin duniya, da ingiza manyan bukatun ci gaban nahiyar tsakanin kasashe masu tasowa.
Cikin jawabinsa na bude taron, shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce taron ya dada fito da muhimmancin bin akida, da tasirin cudanyar mabanbantan sassa. Ya kuma tabbatar da babu wata hanyar warware tarin kalubalen da daukacin al’ummun duniya ke fuskanta sai ta hanyar hadin gwiwa, da hada karfi waje guda da yin aiki tare.
A nasa tsokaci kuwa, yayin da yake jawabi ga mahalarta zaman farko na taron, firaministan Sin Li Qiang, kira ya yi ga gamayyar kasashen na G20, da su zage-damtse wajen marawa juna baya, da nacewa wajen goyon bayan cinikayya cikin ‘yanci, da gina budadden tsarin tattalin arzikin duniya, a gabar da farfadowar tattalin arzikin duniya ke tafiyar hawainiya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














