Duba da canjin yanayi, sanyi ya fara gashi sai da gyara saboda kakkaryewa:
Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo.
Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen dake dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi tsawo da maiko, wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.
Wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, bai kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban, in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Abubuwan da za a bukata:
Man Amla, Zuma Ruwan dumi:
Yadda za a hada:
A zuba cokalin amla biyu a roba, sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla, a sanya cokalin ruwan dumi kamar 2-3. A juya hadin har sai sun cakudu da juna.
Sannan sai a taje gashi kafin a fara shafa wannan hadin a fatar kai. Idan an shafa sai a jira na tsawon minti 30. Sannan a wanke kai da man wanke gashi shampoo.
Amfani da man kwakwa; Man kwakwa na sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafa shi a gashin kai duk lokacin da za a yi kitso ko kuma a riga gauraya shi a cikin man kitso.
Man zaitun; Wannan man na da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma rage furfura a gashi da kuma sanya gashi tsayi da sheki da kuma kyau.
Gyara gashi:
Abubuwan bukata: Man zogale, Man kwakwa, Man zaitun.
Ki hade su ki rinka shafawa a kai.
Gyaran gashi
Man zogale, Ganyan magarya, Kanunfari kadan:
Ki hade ki shafa, yana sa tsawon gashi, yana sanya shi laushi.














