Babbar kotun daukaka kara ta biyu a Jihar Zamfara, wadda mai shari’a Bello Shinkafi ke jagoranta, ta bai wa Kwamishinan Ma’aikatar Gona na jihar umarnin a cikin kwana biyu da ya dawo da tiraktoci 58 da ake zargin ya sayar da su.
Kotun a jiya Ltinin, ta umarci kwamishinan da ya gurfana a gabanta domin yi mata bayanin dalilansa na zuwa ya kwashe tiraktocin duk da maganar na gaban kotu.
- Mutane 8 Sun Mutu A Ruwa A Jihar Jigawa
- An Soma Shari’ar Matashin Da Ya Yi Sanadin Yanke Kafar Wata Yarinya A SakkwatoÂ
Wakilinmu, ya nakalto cewa tiraktocin da ake zargin kwamishinan da sayarwa wata kotu ce ta kama su da nufin yin gwanjonsu don biyan kudin da kamfanin Dunbulun Investment ke bin gwamnatin Jihar Zamfara bashi.
Barista Musbahu Salahudini wanda ya ke kare kamfamin Dunbulum, ya yi wa manema labarai karin bayani akan hukuncin kotun, ya ce a shekara ta 2019 kotun daukaka kara ta uku ta yi hukuncin cewa gwamnatin Jihar Zamfara za ta biya kamfanin Dunbulun Investment kudi Naira miliyan dari biyu da ashirin.
Ya ci gaba da cewa a lokacin gwamnatin ta biya miliyan dari da ‘yan kai saura miliyan dari da uku suka rage ba ta biya ba.
“Hakan ya sa babbar kotun ta uku ta bada umarni kama kaddarorin gwamnatin a lokacin ta kama wasu motocin gwamnatin da taraktoci Ma’aikatar Gona 58 a cikin watan Disamban na bara da nufin a yi gwanjon motocin don a biya kamfanin Dunbulun kudinsa, kotun ta yi ta jan kafa akan batun sayar da kaddarorin,” In ji barista Musbahu.
Barista Musbahu ya kara da cewa, “Dokar ta bai wa mai kara dama idan alkalin da ke shari’a ba zai yi maka adalci ba to ka kai kara ga kotun gaba wannan ne ya bamu damar kai karar ga kotun daukaka kara ta biyu don neman hakkinmu.
“Kuma mun shigar da kara a kotun gaban ne don tilastawa kotu ta uku ta yi gwanjon kayan da aka kama da nufin biyan mu hakkokinmu.
“Ana haka sai muka samu labarin cewa, kwamishinan gona ya kwashe taraktocin 58 ya saida. Akan haka ne muka shigar da kara don mu shaida wa mai shari’a Bello Shinkafi a gaban lauyan gwamnatin aka yi hakan ba wanda ya musa.”
Lauyan ya ci gaba da cewa bayan shigar da kokensu ne ya sanya mai shari’a Bello Shinkafi ya amsa bukatarsu na kwamishinan gona da ya gaggauta kawo taraktoci 58 gaban kotun cikin kwana biyu kuma ya mika kansa a gaban kotun a ranar 14/9/2022, don ya kare kansa akan wasa da shiri’a da ya yi ta yadda motoci na gaban kotun zai kwashe ya sayar.
‘Yan jaridu sun nemi jin ta bakin lauyan gwamnati Jihar Zamfara, inda ya bayyana masu cewa bai fa hurumin yin magana da su sai da umarni kwamishinan shari’a na Jihar.