Gwamnonin Kudu maso Yamma sun sake kira da a kafa ’yansandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a yankin.
Sun yi wannan kiran ne bayan taron sirri da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo.
- Gwamnatin Kano Na Shirin Yi Wa Yara Miliyan 3.9 Allurar Foliyo A Zagaye Na 4
- Gwamnatin Kano Na Shirin Yi Wa Yara Miliyan 3.9 Allurar Foliyo A Zagaye Na 4
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da Babajide Sanwo-Olu (Legas), Dapo Abiodun (Ogun), Lucky Aiyedatiwa (Ondo), Biodun Oyebanji (Ekiti), da mai masaukin baki Seyi Makinde (Oyo).
Mataimakin Gwamnan Osun, Kola Adewusi, ya wakilci gwamnan jihar.
Gwamnonin sun amince a kafa Kudin Tsaro na Yankin Kudu maso Yamma domin ƙarfafa yaƙi da garkuwa da mutane, ta’addanci, haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da kuma shiga jihohi ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar DAWN za ta kula da kudin, tare da sa ido daga manyan mashawartan tsaro na kowace jiha.
Haka kuma, sun amince a kafa wani dandalin bayanan tsaro na yanar gizo domin musayar bayanai, rahotannin hare-hare, da sanarwar barazana a lokaci guda tsakanin jihohin yankin.
Gwamnonin sun nuna damuwa kan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda suka buƙaci sabbin ƙa’idoji da tsaurara hukunci.
Sun kuma roƙi Gwamnatin Tarayya ta tura dakaru domin kare da kuma ƙwato dazuzzukan da ɓarayi da ’yan ta’adda ke buya a ciki.
Taron na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro suka ƙaru a sassa daban-daban na ƙasar, musamman satar mutane, ta’addanci a karkara, da hare-hare a jihohin Neja, Kebbi, Kwara, Bauchi, da Borno.














