’Yan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da mutum 10 a daren Litinin a ƙaramar hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano.
Ɗan uwa ga wasu daga cikin mutanen da aka sace a ƙauyen Biresawa, Kabiru Usman, ya bayyana cewa maharan sun kai farmaki ne kusan ƙarfe 10 na dare, inda suka sace mutane biyar daga kauyen Biresawa, sannan suka tafi da wasu biyar daga makwabcin kauyen Tsundu, wanda ya ce mazauna yankin sun yi ƙoƙarin kare kansu, amma maharan sun fi ƙarfinsu.
- Rashin Tsaro Zai Haifar Da Mummunar Yunwa A Arewacin Nijeriya – Majalisar Ɗinkin Duniya
- Gwamnonin Kudu Maso Yamma Sun Sake Jaddada Buƙatar Kafa ’Yansandan Jihohi
Ya ce tun kafin harin, al’ummar yankin sun sanar da ’yansanda da sojoji bayan samun bayanai cewa ’yan bindigar na kan hanyarsu zuwa yankin amma ba su ɗauki mataki ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yansandan Kano (PPRO), SP Abdullahi Kiyawa, ya ce za su binciki lamarin kafin su fitar da sanarwa a hukumance.
Tun farko jarida LEADERSHIP ta ruwaito cewa ’yan bindigan da ake zargin sun fito daga Jihar Katsina, su ne ke kai hare-hare kan ƙauyukan da ke iyaka da Kano, bayan yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla a garuruwan Ingawa, da Kankia da kuma Kusada na Jihar Katsina a kwanan nan.














