An rufe taron koli na shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 karo na 20, a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu a ranar Lahadi 23 ga wannan wata. An gudanar da taron a nahiyar Afirka, ya kuma samar da fatan bai daya na kasashe masu tasowa na duniya, wajen sa kaimi ga yin kwaskwarima kan tsarin sarrafa harkokin duniya, kana an gabatar da gudummawar Afirka game da raya kungiyar G20 da harkokin duniya baki daya.
A matsayin muhimmiyar mambar kungiyar G20, kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta kiyaye sauraron ra’ayoyin Afirka, da maida hankali ga bukatun Afirka, da kuma nuna goyon baya ga ayyukan Afirka. A halin yanzu, ana samun bunkasar alaka a tsakanin kasa da kasa a fannin tattalin arziki, babu wata kasa da za ta iya rayuwa ita kadai.
Tare da yin kokarin samun zamanintarwa irin na kasar Sin, da kuma aiwatar da kiran sarrafa harkokin duniya, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da sauran kasashe masu tasowa, wajen raya kungiyar G20, da kuma kara shiga aikin sarrafa harkokin tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab Zhang)














