An kammala bikin baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2022 da aka shafe kwanaki 6 ana gudanarwa jiya Litinin.
Yayin bikin na bana, an gudanar da jigon taruka 128 da gabatarwa da shawarwari guda 65, wanda ya kai ga cimma jimillar nau’o’in sakamako guda 1,333 da suka hada da hada-hadar kasuwanci,da zuba jari, da gabatar da yarjeniyoyi da dabarun hannayen jarin kirkire-kirkire da dai sauransu. Yayin da yawan mahalarta taron ya zarce 250,000.
Bikin baje kolin CIFTIS na wannan shekara, ya kasance mafi girma a ma’auni da kuma kimar habaka kasashen duniya.
A ranar rufe bikin baje kolin, mataimakin darektan ofishin gudanarwa na hukumar baje kolin ayyukan ba da hidima, kuma daraktan ofishin kasuwanci na birnin Beijing, Ding Yong, ya sanar da cewa, bikin baje kolin, ya jawo hankalin manyan kamfanoni 507 dake kan gaba a duniya don halartar bikin a zahiri, yayin da a karon farko aka gabatarwa kamfanoni da cibiyoyi da sabbin samfura fiye da 100, da sabbin fasahohi da nasarori a fannonin kwaikwayon tunanin dan-Adam.
“An sanya sabuwar rukunin kungiyar ciniki ta Global Service Trade Alliance, a matsayin kungiyar hadin gwiwa ta kasa da kasa, kana an gudanar da taron ‘yan kasuwa masu samar da ayyukan hidima na duniya.
A karon farko kasashe 10 da suka hada da hadaddiyar daular Larabawa da Switzerland, sun shirya nune-nune da sunan kasashensu, da yawan nune-nunen da aka gudanar a taro, da sunan kasa ko hedkwatar kungiyar kasa da kasa.
An samu karin zaman taruka 13 fiye da na baya, yayin da yawan ayyuka masu alaka da kasashen waje ya kai kaso 20.8 cikin 100, wanda ya shafi manyan kasashe da yakuna 27 cikin 30 dake kan gaba a fannin hidimar cinikayya, ta haka muna iya ganin yadda bikin baje kolin ya kara fadada rukunin abokan cinikayyar kasa da kasa. (Ibrahim)