A bana ake cika shekaru 10 da kulla yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, inda duniya ta shiga wani sabon mataki dangane da jagorancin matakai da ake dauka na dakile kalubalen sauyin yanayi. Hakan ne ma ya sa a yayin taron MDD na sauyin yanayi karo na 30 da ya gudana a birnin Belem na kasar Brazil a baya bayan nan, aka dora muhimmancin gaske ga manyan batutuwan da suka shafi kana, inda aka karfafa kira ga sassan kasa da kasa da su yi aiki tare wajen lalubo dabarun magance sauyin yanayi, da gaggauta rage fitar da nau’o’in hayaki masu dumama yanayi, da matakan karfafa juriyar sassan kasa da kasa ga illolin sauyin yanayi, da ma ingiza tafiya tare, da kuma sauyi zuwa dabarun kyautata yanayi na bai daya.
Duk da koma baya daga wasu kasashen duniya game da nauyin da ya kamata su sauke a wannan tafiya, kasar Sin ta yi gaba wajen aiwatar da managartan manufofin jagoranci, da suka sanya ta a sahun gaba ta fuskar sauke nauyi da hakkin da ya rataya a wuyanta.
A matsayinta na babbar kasar mai hangen nesa da dattaku, Sin ta rungumi manufar kasancewar kasashe masu mabambantan tasiri a duniya, tana ta zurfafa hadin gwiwa, da aiki tukuru wajen gina tsarin cimma matsaya guda a fannin yaki da sauyin yanayi. Har ila yau, kasar Sin ta himmatu wajen ingiza matakan da suka dace duniya baki daya ta aiwatar, don shawo kan wannan kalubale na sauyin yanayi.
Hakan zai fito fili idan muka waiwayi jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar shekaru goma da suka gabata, yayin taron sauyin yanayi na Paris. A lokacin ya yi kira da babbar murya da a yi amfani da yarjejeniyar wajen cimma nasarar tsare-tsaren aiki na MDD, da fayyace taswirar sauya tafiya zuwa dabarun ci gaba marasa gurbata yanayi da sai sauran matakai masu nasaba.
A cikin gida kuwa, Sin ta yi aiki mara iyaka, wajen tabbatar da ta bayar da isasshiyar gudummawar cimma burikan magance sauyin yanayi. Karkashin hakan a shekarar 2009, Sin ta sanar da burinta na rage fitar da hayakin carbon zuwa shekarar 2020 bisa radin kanta. Ta kuma cimma wannan buri kafin ma cikar wa’adin. Kazalika, a watan Yunin shekarar 2015, Sin ta sanar da takamainan matakanta na cimma nasarar yarjejeniyar Paris wato NDC zuwa shekarar 2030.
Sin ba ta tsaya a nan ba, inda a watan Satumban bana, ta sake fitar da kudurorinta na NDC na nan zuwa shekarar 2035, masu kunshe da aniyar kara rage fitar da iskar carbon bisa babban matsayi, da fadada kudurori masu nasaba da hakan a dukkanin fannonin tattalin arzikin kasa.
Da wadannan matakai da ma wasu karin manufofin, Sin ta martaba aniyarta, ta kuma nuna matsayinta na babbar kasa mai tasowa, wadda duniya ke kara martabawa bisa nauyin da take saukewa ta hanyar aiwatar da matakai na zahiri, da hadin gwiwa tare da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, ta yadda duniya za ta kubuta daga mummunan tasirin sauyin yanayi, a kuma gudu tare a tsira tare.














