A yayin da matsalolin tsaro ke kara kamari a Arewacin Nijeriya, kungiyar Tuntuba ta Arewa (Arewa Consultatibe Forum) ta gudanar da taron bikin cikar ta shekaru 25 da kafuwa, inda ta tattauna kan matsalolin tsaro, ci gaban yankin da kuma hanyoyin da za a bi domin inganta zaman lafiya.
Duk da zaman zullumi da tashin kwanciyar hankali sakamakon sace zaliban makarantu a jihohin Kebbi da Neja bai hana kungiyar dattawan Arewa gudanar da taron ba inda taron ya mayar da hankali kan batun tsaro da makomar yankin Arewa.
- G20: Kaduna Ce Jihar Da Tafi Dacewa Da Zuba Jari A Nijeriya – Gwamna Uba Sani
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Naira Biliyan 878 A Matsayin Kasafin 2026
A yayin taron wanda ya gudana a Jihar Kaduna, kungiyar ta ACF ta bayyana takaici da damuwarta dangane da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a yankin Arewa.
Tun farko da yake jawabi Shugaban Majalisar Amintattu na kungiyar Alhaji Bashir M. Dalhatu, Wazirin Dutse, ya koka dangane da yadda yankin arewa ya zamo tamkar filin yaki, inda ake kisa da yin garkuwa da mutane a kullum, inda yace lallai wannan abin takaici ne da ya zama dole a dauki mataki akai.
Ya kuma jaddada aniyar kungiyar na samar da hazin kai da bin ka’idojin gudanarwa tsakanin mambobin kungiyar domin bayar da gudunmawar da ta kamata wajen ciyar da yankin gaba.
Alhaji Dalhatu ya jaddada bukatar daidaito da taka-tsantsan wajen isar da sako ga jama’a musamman ga jami’an kungiyar da ke hulda da kafafen watsa labarai gabanin babban zaben 2027.
Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin wadannan kungiyoyi “barazana ga hazin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro.
Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “aungiyoyin marasa kishin kasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani.
A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri.
A jawaban da suka gabatar a wajen taron manyan Attajiran nan biyu daga jihar Kano Alhaji Aliko Dangote d Abdulsamad Isiyaka Rabi’u, sun bayyana yadda matsalar tsaro ke shafar harkar kasuwanci a Arewa, inda suka bukaci ‘yan arewa da su bayar da dukkanin gudummawar da ta kamata wajen shawo kan matsalar.
A jawabin Shugaban kasa Tinubu wanda ya samu wakilcin shugaban majalisar dokokin tarayya Abbas Tajuddeen ya bayyana damuwarsa kan yadda harkar tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Arewa, inda ya bayyana aniyar gwamnati na daukar matakan gaggawa domin shawo kan matsalar.
A zantawarsa da wakilinmu jim kadan bayan kammala taron, Shugaban Rundunar Talakawan Nijeriya Malam Imrana Nas, ya bayyana cewa akwai bukatar Dattawan arewa su dage wajen Samar sa gwamnati irin halin sa yankin Arewa take ciki musamman a bangare matsalar tsaro sa talauci da rashin aikinyi.
Ya baya da kokarin kungiyar ya ACF wajen tattaro manyan ‘Yan Arewa domin tattauna matsalolin da suka shafi ci gaban yankin.
Imrana Nas ya bayyana craw gwamnati ba ta nuna cikakkiyar shirye-shiryen kawo karshen matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya ba, duk da karuwar hare-haren ’yan bindiga da ta’addanci a yankin.
Imrana Nas ya ce hare-haren da ake ta fama da su a ya kin sun nuna cewa tsarin yaki da ’yan ta’adda bai kai matsayin da ake bukata ba. Ya ce idan ana son a magance matsalar gaba daya, sai an zarce matakan da ake dauka yanzu.
Ya nuna rashin gamsuwarsa akan matakan da ake dauka wajen yin sasanci da ‘yan ta’adda Inda yace akwai lauje cikin nadi .
“ Wadanan mutane da ake kira da ‘Yan ta’adda basu fi karfin gwamnati ba kuma baza su fi karfin gwamnati ba sai dai akwai lauje cikin nadi wannan halin ya sa aka barsu suke yin abinda suke so amma fa ba don gwamnati bazata iya maganinsu ba. Nayi imani da Allah da kasar Yarabawa ne ko Inyamurai da baza su amince ba da tuni ankai karshen wannan fitinar. Mu yanzu idan gwamnati ba zata iya ba to zamu hadu ci gaba da kumumuwar addu’a kamar yadda mukayi kamin zuwan Buhari shugaban kasa “
“ Yanzu Fa dan ta’adda ne zaizo ayi sasanci da shi da bindigar shi zaizo a gama sasanci kuma ya dauki bindigarshi ya koma da ita, wai mutumin da kake nema ruwa a jallo sai gashi yazo inda kake kuma kun gama magana ya koma kaga ba’a shirya maganin wadannan mutanan ba; ba’a shirya fada dasu ba”
Imrana Nas ya kara da cewa matsalar tana da tushe mai zurfi, ciki har da talauci, da taoron Mutuwa, su kuma shugabanni sun komai san duniya duk da irin makudan kudazen da ake warewa a harkar. Ya ce dole gwamnati ta karkata hankali wajen addu’a tunda alamu sun nuna gwamnati kamar bazata iya ba.”
A yanzu haka, al’ummar Arewa na ci gaba da fatan gwamnati ta kara daukar matakai masu karfi domin dakile ayyukan ta’addanci, yayin da suka bayyana damuwa kan yadda matsalar ke kara ta’azzara a wasu yankuna.
Taron dai ya samu halartar manyan jama’a daga dukkanin fadin arewacin Nijeriya harda makwabta inda a karshen taron a karrama wasu manyan ‘yan arewa wadanda suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da Namadi Sambo da Dangote da Isiyaka Rabi’u da sauran jama’a da dama, inda aka tara kudi sama da Naira Biliyan 90
Masana tsaro da suka yi jawabi a taron sun yi bayanin cewa karuwar hare-haren ’yan bindiga da rawar da wasu tsageru ke takawa wajen sace-sacen dalibai abu ne mai nassaba da karancin kayan aiki, rashin wadatattun jami’an tsaro da kuma rashin tsarin kula da iyakokin Arewa.














