Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ranchers Bees ta jihar Kaduna ta amince da filin wasa na Bako Kontagora da ke Minna a matsayin sabon filin wasanta na gida, sakamakon gyare-gyaren da ake yi wa filin Kaduna Township. Wannan na zuwa ne bayan ƙungiyar ta fara kakar gasar NNL ta bana da wasa a Kaduna, kafin gwamnati ta rufe filin domin ci gaba da aikin sabuntawa.
Ranchers Bees za ta karɓi Bichi First a wasan gida mai zuwa a Minna, sannan a ƙarshen mako za ta fafata da Kebbi United a filin FIFA Goal Project da ke Birnin Kebbi. Ƙungiyar na fatan ganin wannan sabon tsari zai taimaka mata wajen komawa gasar Firimiya ta Nijeriya, bayan dogon lokaci tana fafatawa a matakin rukunin ƴan dagaji.
- Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
- NNL: An Ci Tarar Kungiyar Mailantarki FC Naira Miliyan Daya Kan Rashin Da’a
Rahotanni sun nuna cewa sabon tsarin gudanar da wasannin na Ranchers Bees ya zo ne bayan sauyin mallaka, inda fitaccen ɗan wasan Super Eagles, Sadiq Umar, tare da haɗin gwuiwar ɗan majalisar tarayya Bello El-Rufai suka saye ƙungiyar daga hannun iyalin marigayi Alhaji Muhammad Mukhtar Aruwa a watan Agustan da ya gabata. Wannan sauyi ya ƙara ɗaga muradin farfaɗo da martabar ƙungiyar.
Masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa sun yi maraba da wannan mataki, suna ganin cewa filin Bako Kontagora zai ba Ranchers Bees ingantaccen wuri na buga wasanni, musamman duba da kyawawan kayan aiki da kuma amincin filin. Ana sa ran sabon yanayin zai ƙarfafa ƙungiyar wajen cimma burinta na dawowa sahun manyan ƙungiyoyi a gasar NPFL.














