Saudiyya Arebiya ta fadada damar da mutane ke da ita na ciniki da kuma kwankwadar barasa ga mazauna kasar wadanda ba Musulmai, abin da ke nufin a yanzu an kara yawan shagunan hada-hadar barasar sabanin guda daya tal da ake da shi, wanda ke a birnin Riyadh fadar gwamnatii da aka samar tun farko domin jami’an Diplomasiyya.
Rahotanni sun ce cikin sirrin gwamnatin kasar Saudiyya ta yi aikin fadada shagunan musamman a unguwannin jami’an diplomasiyyar da ke zaune a birnin na Riyadh.
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Uku Bayan Rufe Makarantu A Adamawa
- Dogaro Da Noman Gargajiya Kadai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Ba – Farfesa Rabi’u
Ana ganin cewa wannan mataki baya rasa nasaba da yadda sannu hankali damar sha da kuma samun barasa cikin sauki ke bai wa ‘yan yawon bude ido kwarin gwiwar ziyartar kasar ta yankin Gulf mai tsauraran dokokin addinin Islama da suka haramta kusantar barasa.
Mahukuntan Saudiyya dai na bukatar janyo hankalin baki ‘yan yawon bude ido akalla miliyan 150 nan da shekarar 2030, yayin da ake ganin yadda kasar ke ci gaba da zuba jari a bangarorin otel-otel da wuraren shakatawa.
Bayanai sun ce baya ga jami’an diplomasiyya, ma’aikata ‘yan kasashen ketare da ke aiki kuma suke samun albashin da ya kai SAR dubu 80 dai-dai da Dalar Amurka dubu 21 a wata na damar siya da kuma shan barasar amma bisa sanya idanun gwamnati.
Rahotanni sun ce a yanzu al’ummar kasashen ketare mazauna Saudiyya da a baya ke da sassaucin sarrafa barasar ta gargajiya a gida su kuma sha abinsu amma ba tare da sayarwa ba, na da damar neman lasisin hukuma don fara cinikin barasar a hukumance.
Matakin na sassaucin sha da ta’ammali da barasar na a karkashin tsare-tsaren gwamnatin Saudiya na fasalta dokokinta don yin dai dai da zamani karkashin shirin BISION 2030 da Yarima mai jiran gado na Saudiyan ke jagoranta, wanda ya sahale bude gidajen kallo na Cinema da kuma bai wa mata damar tuki da ma bunkasa bangarorin nishadi da yawon bude ido.














