Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya jaddada cewa Nijeriya ba za ta samu ci gaba na haƙiƙa ba sai an bai wa mata cikakken damar shiga al’amuran mulki.
Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron horaswa da Magnetite Foundation tare da haɗin gwiwar M2Paramount Foundation suka gudanar a ranar Asabar.
- Saudiyya Ta Sake Sassauta Dokokin Ta’ammali Da Barasa A Cikin Kasar
- Morocco: Kasar Da Ke Neman Zama Fuskar Kwallon Ƙafa A Duniya
Taron, mai taken “EMPOWER HER”, an shirya shi ne domin ƙarfafa wa ‘yara mata masu zuwa makarantar sakandare damar samun ƙwarewa a sana’o’i daban-daban.
Hajiya Jidda Usman, Shugabar Magnetite Foundation, ta bayyana cewa an ƙirƙiro wannan shiri ne saboda mawuyacin halin tattalin arziƙi da rashin tabbas da ‘yan mata da yawa ke fuskanta bayan kammala makarantar sakandare.
Hakazalika, Adam Muhammad, Shugaban M2Paramount Foundation, ya ce shirin zai taimaka wa mahalarta fahimtar rawar da za su iya takawa wajen bunƙasar ƙasar baki ɗaya.
Taron ya samu halartar ‘yan mata da dama daga makarantu daban-daban a Kano da kewaye.
Mahalarta sun samu horo, jagoranci, da tallafi, inda aka zaɓi waɗanda suka fi ƙwazo domin samun ƙarin tallafi don gina sana’o’i masu ɗorewa.














