Al’Amma daga yankin Unguwar Tsamiya a Faruruwa da Dabawa dake cikin ƙaramar hukumar Shanono ta shiga firgici bayan wasu ƴan bindiga sun mamaye yankin da dare a ranar Lahadi, inda suka yi garkuwa da aƙalla mutum 25 tare da jikkata wasu biyu. Harin ya zo bayan kwana guda da makamancin harin da aka kai Yan Kamaye a Tsanyawa, inda aka sace mutane uku.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kutsa cikin garin ne da tsakar dare, suna harbe-harbe domin razana jama’a kafin su tafi da mutane da dama. Wannan ya sake tayar da hankulan mazauna yankunan kan iyakar Kano da Katsina, musamman ganin yadda hare-haren ke ƙara yawaita cikin makonni.
- Buƙatar Daƙile Kutsen ‘Yan Bindiga Na Iyakokin Jihar Kano
- Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Sun Yi Mubayi’a Ga Khalifa Sharif Saleh
Mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Shanono, Ammar Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce har yanzu ana tattara sahihan bayanai kafin a fitar da cikakken jawabi daga hukumomi. Ya ce bincike na ci gaba don tantance adadin mutanen da aka sace da wadanda suka ji rauni.
Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda hare-haren ke ƙara matsowa cikin Jihar Kano duk da tabbacin da hukumomi ke bayarwa game da tsaro. Wasu sun yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su ƙara kai ɗauki domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankali.














