ASUU ta fitar da wani rahoton nasarori da ta samu kan takaddamar yarjejeniyarta da gwamnatin tarayya ta 2009, inda ta samu sabbin alƙawurra kan ‘yancin kai na jami’o’i, kuɗaɗe, shugabanci, albashi da walwalar ma’aikata.
Kungiyar ta ce ɓangarorin biyu sun amince da cikakken ‘yancin kai, aiwatar da dokokin da ake da su kan Majalisar Gudanarwa, tabbatar da nadin mataimakin shugaban jami’a (VC) bisa cancanta da kuma ba da damar gudanar da zaɓuka na cikin gida don shugabancin sashe da malamai.
- Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Shugaban Laos Kan Cika Shekaru 50 Da Kafuwar Kasar
- Gobara Ta Yi Ajalin Mutum 5 ‘Yan Gida Ɗaya A Jihar Katsina
A cikin wata sanarwar manema labarai, da shugaban kungiyar Christopher Piwuna ya sanya wa hannu, ta amince cewa, karatuttukan kafin digiri za su takaita ne ga fannonin kimiyya, kuma yanzu za a riƙa yin ƙarin girma ne bisa ga sakamakon binciken da malami ke yi. Za kuma a cire wa jami’o’i harajin shigo da kayayyakin karatu.
Kwamitin aiwatarwa da sashin sa ido na NUC zai kula da aiwatar da wannan yarjejeniyar, tare da yin bita a duk bayan shekaru uku. ASUU ta amince da tsarin albashi da aka gyara wanda ya yi daidai da shawarar Nimi Briggs, yayin da za a biya alawus-alawus da aka samu kowace shekara a kashi 12% na kudin albashin kowace jami’a. An kuma amince da wani sashe na rashin cin zarafin malamai.
Wannan sanarwar ta fito ne daga shafin sada zumunta na kungiyar a ranar Talata, 2 ga Disamba, 2025 da tsakar rana.














