Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Babban Hafsan Tsaro (CDS), Janar Christopher Gwabin Musa (Rtd), a matsayin sabon Ministan Tsaro.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya yi murabus a ranar Litinin, 1 ga Nuwamba, 2025, saboda dalilai na rashin lafiya.
- ASUU Ta Yi Nasarar Cimma Manyan Buƙatunta Na Yarjejeniyar 2009 Da Gwamnati
- An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, ta ce, a cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya isar da nadin Janar Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Badaru.
Janar Musa, wanda zai cika shekaru 58 a ranar 25 ga Disamba, soja ne mai hazaka wanda ya yi aiki a matsayin Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa Oktoba 2025.
An haife shi a Sokoto a 1967, Janar Musa ya sami karatunsa na firamare da sakandare a can sannan ya halarci Kwalejin Ci Gaba da karatu a Zariya. Ya kammala karatun a shekarar 1986 sannan ya shiga Kwalejin Tsaron kasa (NDA) a wannan shekarar, inda ya sami digirin farko na Kimiyya bayan kammala karatunsa a shekarar 1991.














