Uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, Peng Liyuan, da uwargidan shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, Brigitte Macron, sun ziyarci gidan wasannin kwaikwayo ta al’umma ta Beijing, wato BPAT.
Brigitte ta yi rakiya ce ga shugaban Faransa a ziyarar aiki da ya kawo kasar Sin.
A gidan nune-nunen kayan tarihi na BPAT, Peng Liyuan da Brigitte Macron sun samu cikakkiyar fahimta game da ci gaban da BPAT ya samu da kuma mu’amalarsa da masu wasannin kwaikwayo na kasar Faransa.
Yayin da take nuni da cewa, Sin da Faransa manyan kasashe ne masu al’adu na gado, Peng Liyuan ta bayyana fatan cewa, masu fasaha daga bangarorin biyu za su karfafa mu’amala da koyon ilimi daga juna, da samar da karin fitattun ayyukan fasaha.
A nata bangaren, Brigitte Macron ta bayyana aniyarta ta inganta huldar jama’a da mu’amalar al’adu tsakanin kasashen biyu, da kara bunkasa fahimtar juna da abokantaka a tsakanin al’umma. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














