Kamfanin hakar danyen mai a teku na Sin, ya sanar da fara aiki a mataki na biyu, na hakar danyen mai a rijiyoyin yankin Liuhua, wadanda su ne mafiya zurfin teku da kasar ta Sin ke hakar mai daga gare su. Matakin ya nuna yadda Sin ta cimma nasarar samar da damar hakar danyen mai, da iskar gas daga sassan yankin teku mai zurfi.
Yankin hakar mai a teku na Liuhua, yana sashen kogin Pearl, wanda kuma shi ne yankin hakar mai na teku mafi girma dake da tarin danyen mai da za a iya haka. Tun bayan fara aiki a yankin a shekarar 1996, rijiyoyin man wurin sun samar da gangar danyen mai sama da tan miliyan 20.
To sai dai kuma, bincike ya nuna yadda wurin ke kunshe da kimanin tan miliyan 140 a can kasan yankin farko na hakar mai, wanda hakan ya wajabta gudanar da mataki na biyu na aikin hakar mai a wurin.
Aikin a mataki na biyu, ya kunshi haka tagwayen rijiyoyin mai, wato Liuhua 11-1 da Liuhua 4-1, wadanda matsakaicin zurfinsu ya kai kimanin mita 305. Wadanda za su samar da rijiyoyin fitar da danyen mai har 32. (Saminu Alhasan)














