A ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937, dan kasar Jamus John Rabe, ya rubuta cikin kundin adana bayanansa cewa, “an sake jefa boma-bomai masu dimbin yawa, sa’an nan, a kan hanyarmu ta zuwa titin Shanghai, ko ina ana iya ganin gawawwakin fararen hula. A gabanmu, mun ga dakarun mamaya na kasar Japan.”
Cikin kundin, John Rabe ya rubuta ta’asar da sojojin Japan suka aikata a birnin Nanjing na kasar Sin, a ranar 13 ga watan Disamban shekarar ta 1937, hakan ya sa kundin ya kasance muhimmiyar shaida, da ta fayyace gaskiyar kisan kiyashin birnin Nanjing.
Dakarun mamaya na kasar Japan sun hallaka Sinawa 300,000, tare da cin zarafin mata masu dimbin yawa. Kazalika yara da yawa sun rasa rayukansu, kuma an rusa kaso 1 bisa 3 na daukacin gidajen birnin, tare da kwashe dukiyoyi masu dumbin yawa. Kisan kiyashin birnin Nanjing da dakarun mamaya na kasar Japan suka aikata, ya zama laifin cin zarafin dan Adam, kuma babu wanda zai iya musanta wannan lamari, ganin yadda aka tattara shaidu masu karfi dake tabbatar da aukuwarsa.
To sai dai kuma ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Japan ta ki amincewa da kuskuren da ta aikata na tayar da yaki, maimakon hakan ma, ana iya ganin masu aikata laifuffukan tayar da yakin suna dawowa teburin siyasar Japan, kana shugabanni, da manyan jami’an kasar da dama suna kai ziyara haikalin Yasukuni, inda suke girmama kaburburan mayakan da suka jagorancin aikata wancan ta’asa.
A farkon watan Nuwamban bana, firaministar kasar Japan Takaichi Sanae ta bayyana cewa, matsalar Taiwan tana da alaka da tsaron kasar Japan, inda ta nuna cewa, mai iyuwa ne kasar Japan ta dauki matakan soja, wajen tsoma hannu cikin harkokin Taiwan na kasar Sin. Wannan tsokacin da ta yi, ya yi kama da tsohuwar dabi’ar kasar Japan ta amfani da karfin soji.
Watsi da tarihi cin amana ne kana kin amincewa da aikata laifi tamkar sake aikawa ne. A bana, ake cika shekaru 80 da Sinawa suka samu nasara a yaki da maharan Japan da ma yakin duniya na II, kuma ba zai yiwu a musanta kisan kiyashin birnin Nanjing ba. Abubuwan da Takaichi Sanae, da ma sauran ‘yan siyasa da dama na kasar Japan suka aikata na musantawa da kokarin gyara tarihi, sun kasance laifi na farfado da dabi’ar Japan ta amfani da karfin soji, lamarin da ya illata dokar kasa da kasa, tare da gurgunta nasarar da aka cimma a yakin duniya na biyu, kana ya bakanta ran gamayyar kasa da kasa. Tabbas, tarihi zai wanzar da cewa, adalci, da haske, da kuma ci gaba, za su yi galaba kan yaki da rashin adalci, da duhu, da kuma tashe-tashen hankula! (Mai Fassara: Maryam Yang)














