A yau Alhamis, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya kaddamar da hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki game da samar da kayayyaki masu alaka da shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2026 wanda CMG din zai shirya, inda aka kuma kaddamar da mutum-mutumin doki guda hudu masu alamta shagalin, wanda CMG kan shirya a kowace shekara don murnar bikin bazara, wato bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta Sinawa, kuma bisa al’adar Sinawa, shekarar 2026 za ta kasance ta doki. Wani babban jami’in CMG, Peng Jianming ya halarci bikin, inda tare da sauran wasu baki suka kaddamar da kayayyaki masu alaka da shagalin bikin bazara na CMG.

An sanya wa mutum-mutumin doki nan hudu sunayen “Qiqi”, “Jiji”, “Chichi”, da “Chengcheng”, wadanda cike suke da fara’a da kuzari, wadanda sunayensu suka dace da taken bikin, wato “Ba za a iya dakatar da gudun dawaki ba”. An kuma tsara alamomin dawakin hudu ne bisa hotunan dawakin gargajiya na Sin a lokuta daban-daban, masu cike da kyawun tarihi mai cike da karsashi, da kuma sabon yanayin zamani, da kuma kyakkyawar ma’anar cimma nasara, da kuma burin samun kyakkyawar makoma.














