Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Farfesa Ibrahim Abdullahi Tsafe a matsayin sabon Shugaban Jami’ar Zamfara ta Talata Mafara (ZAMSUT), domin yin wa’adi guda na shekaru biyar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar 16 ga Disamba, 2025, inda ya bayyana cewa naɗin ya biyo bayan shawarwarin Majalisar Gudanarwar Jami’ar.
- Tinubu Zai Gabatar Da Daftarin Kasafin Kuɗin 2026 Ga Majalisun Tarayya
- Kamfanonin Sin Da Zimbabwe Za Su Yi Hadin Gwiwa Wajen Kera Na’urorin Wutar Lantarki
Sanarwar ta ce, Farfesa Tsafe kwararren malami ne mai gogewa, wanda ya kammala digirin digirgir (PhD) a shekarar 2006, sannan aka ɗaga shi zuwa matsayin Farfesa a shekarar 2013 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
A tsawon aikinsa, ya riƙe manyan muƙamai na shugabanci a fannin ilimi, ciki har da zama Dekan Kwalejin Chemical and Life Sciences a UDUS.
Tun daga shekarar 2018, Farfesa Tsafe ya kasance Farfesan wucin-gadi a Jami’ar Zamfara, inda a halin yanzu yake riƙe da muƙamin Dekan na Kwalejin Kimiyya.
Gwamnati ta bayyana cewa kwarewarsa da saninsa na harkokin ilimi za su taimaka wajen ɗaga martabar jami’ar da kuma bunƙasa fannonin koyarwa da bincike.
Gwamna Lawal ya nuna yaƙinin cewa sabon Shugaban jami’ar zai yi anfani da gagarumar gogewarsa wajen kai ZAMSUT zuwa wani mataki mafi girma, daidai da ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa ilimi da tabbatar da nagartar aikin ilimi a faɗin jihar.














