Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce Sin na kira ga Japan, da ta kauracewa kalubalantar ginshikin dokar kasa da kasa, ta hanyar bijiro da burin mallakar makaman nukiliya. Guo ya yi tsokacin ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai na yau da kullum da aka saba gudanarwa, bayan da wani babban jami’in Japan ya furta cewa, kamata ya yi a ce Japan din ta mallaki makaman nukiliya.
A martanin nasa, Guo Jiakun ya ce hargowar baya bayan nan da ake ji daga wasu mahukuntan Japan, dangane da mallakar makaman nukiliya, na kara haskawa duniya karuwar burin masu ra’ayin rikau na Japan, na farfado da amfani da karfin soji, da ballewa daga odar duniya, da gaggauta farfado da karfin sojin kasar.
Daga nan sai jami’in na Sin, ya ce a bana ne aka cika shekaru 80 da cimma nasarar da Sinawa suka yi kan mamayar Japan, da yakin duniya na kin jinin danniya. Kuma lokaci ne da ya kamata Japan ta zurfafa karatun baya dangane da laifukan da ta tafka a tarihi, ta kiyaye dokokin kasa da kasa da na kundin tsarin mulkinta, ta dakatar da bullo da wasu dalilan na fadada karfin soji, tare da dakatar da kalubalantar ginshikin dokar kasa da kasa ta hanyar bijiro da burin mallakar makaman nukiliya. (Saminu Alhassan)














