Idan mace na fama da wadannan matsalolin kamar haka to ta Jarraba wannan maganin In sha Allahu za ta samu waraka.
1.Matsanancin ciwon sanyin mara.
2. Kananan kuraje da ke fitowa mace da sauransu
3. Mace me fitar da farin ruwa.
4. Warin gaba.
5.Me Yawan ciwon mara duk lokacin al’adarta.
Duk macen dake fama da wa’dannan Matsalolin to ta nemi:
Kanwa cokali (3), gishiri cokali biyu (2), tafarnuwa dunkule daya (1)
Saita zuba ruwa dai-dai yadda za ta iya shiga cikin baho ta zauna, sai ta dafa shi idan ya dahu sannan ta Juye shi a baho, ya dan sha iska ya cire Sirace sai ta shiga ciki ta zauna, na tsawon minti 10 zuwa 15 haka.
Ta yi hakan kamar na tsawon sati biyu. To lallai za ta sha mamakin yadda za ta ga cutar sanyi ke fita, sannan in tana son ya zama ta raba da wadancan Matsalolin gaba daya, to sai ta kara da wannan kuma bayan ta yi wancan na farkon.
Abubuwan da ake bukata:
Man Zaitun kwalba daya (1), Man Tafarnuwa kwalba daya (1), Man kwakwa kwalba daya (1)
A hada su a kwano daya a soya su amma za a soya ne da tafarnuwa dunkule daya, In ya soyu sai a sauke shi a barshi ya huce ya yi sanyi sosai, sannan a juye a roba, sai a nemi auduga. Sai a sawa audugar wancan mai ya jiku da man, sannan a daukar a sanya ta agabanta, ba za ta cire ba har sai an ji fitsari ko bayan gida ya taso, sannan sai a cire.
Lalle mace Inta jarraba wannan za ta sha mamakin yadda za taga wani mummunan abin da zai fita ajikinta, sannan za ta ga tana fitar da wani yellown ruwa ko taga wani bakin ruwa yana fita In ta zo fitsari, to alamar sanyin ya fita ajikinta kenan kwata-kwata.














