Shugaba Bola Tinubu ya isa Jihar Bauchi a ranar Asabar domin jajanta wa iyalan fitaccen addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin karfe 4:10 na yamma, inda Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da sauran manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.
Daga nan Shugaba Tinubu ya je Masallacin Sheikh Dahiru Bauchi, inda aka binne shi, domin yi masa addu’a.
ADVERTISEMENT
Sheikh Dahiru Bauchi, jagoran ɗariƙar Tijjaniyya, ya rasu a watan da ya gabata yana da shekaru 92.
Ga hotunan ziyarar a ƙasa:
























