Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Edo ta kama wani mutum mai shekaru 49 bisa zargin kashe dansa mai shekaru 15 da kuma binne gawar a asirce a cikin harabar gidansu a Unguwar Uhe, Karamar Hukumar Igueben ta Jihar Edo.
Kakakin rundunar, Eno Ikoedem, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ta ce lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Disamba.
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- Yadda Ake Funkason Fulawa
Ta ce daga bisani an tono gawar domin ci gaba da bincike bayan mahaifiyar wanda ake zargi, wadda ita ce kakar marigayin, ta ba ‘yansanda bayanai masu amfani.
Sanarwar ta ce, “Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Edo ta kama wani mutum mai shekaru 49 bisa zargin kisan dansa mai shekaru 15 da kuma binne gawarsa a asirce a cikin harabar gidansu a Unguwar Uhe, Karamar Hukumar Igueben ta Jihar Edo.”
“Ranar 6 ga Disamba, 2025, bisa sahihan bayanai, jami’an tsaro karkashin jagorancin Dibisional Police Officer suka tafi wurin da abin ya faru, inda aka tabbatar da sahihancin bayanan.
“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargi ya daki dansa da sanda a ranar Juma’a, 5 ga Disamba, 2025, da misalin karfe 7:00 na yamma, lamarin da ya jawo mutuwar yaron.
“Bayan haka, wanda ake zargin ya haka kabari a cikin harabar gidan ya binne gawar. Kakar marigayin, wadda ita ce mahaifiyar wanda ake zargi mai shekaru 82 da ke zaune a gidan, ta ba ‘yansanda bayanai masu amfani.
“Bayan kammala ka’idojin gudanarwa da suka dace, an tono kabarin, an dauki hotuna, sannan an kwato sandar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin a matsayin hujja. An kama wanda ake zargi kuma yana hannun hukuma yayin da bincike ke gudana.”
Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Edo, Monday Agbonika, ya umarci a mika shari’ar zuwa Sashen Kisan Kai na Sashen Binciken Laifuka na Jihar domin cikakken bincike da gurfanarwa a gaban kotu.
Ya yi gargadi kan dukkan nau’o’in tashin hankali tare da rokon mazauna yankin da su rika gaggauta kai rahoton duk wani abin da ake zargi zuwa ofishin ‘yansanda mafi kusa.













