Dorawa, itace mafi albarka da ke taimakawa wajen warkar da cututtuka iri daban-daban, kama tun daga kan Ganyensa, Sassakensa, Kaucinsa, Saiwarsa, Furensa (Tuntu), ‘Ya’yansa (Kalwa), Garin ‘ya’yansa (Garin Dorawa) da kuma Makuba.
Kowanne a cikinsu, magani ne na musamman.
- Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi
- An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Ganyen Dorawa:
1-Cutar Asma: Ana shan garin Ganyen Dorawa rabin cokali a ruwan dumi, yana maganin Asma kaifiyan.
2-Cututtukan Fata: Ana dafa danyen Ganyen Dorawa a yi wanka da shi da ruwan dumi, yana maganin cututtukan Fata daban-daban.
Sassaken Dorawa:
1-Ga masu saurin jin fitsari: Wanda ke fama da cutar yawan yin fitsari akai-akai, ya nemi Sassaken Dorawa ya dafa ya rika sha, zai rabu da wannan matsala da izinin Allah.
2-Matsalar Zafin Ciki: Ga wadanda cikinsu ke yawan daukar zafi koda-yaushe, sai su sha garin Sassaken Dorawa sau daya a rana, har tsawon kwana uku.
Saiwar Dorawa:
1-Maganin Sanyi: Ana dafa saiwar Dorawa da jar kanwa a sha sau daya, tsawon kwana uku. Tana maganin sanyi kwarai da gaske.
2- Kurga: Ana dafa saiwar dorawa, bayan ta huce ya koma mai dan dumi, sai a tsuma yaro a ciki, yana maganin Kurga yadda ya kamata.
Bawon Dorawa:
1-Maganin Tari: Ana dafa bawon Dorawa guda daya tak da ruwa lita biyu a sha karamin kofi sau daya a rana, idan an tashi sha, sai a zuba zuma cokali daya a sha kofi daya kullum, har ya kare. Cikin ikon Allah, kowane irin Tari ne za a rabu da shi.
2-Ciwon Basir: Ana amfani da Garin Bawon Dorawa mai laushi, a sha karamin cokali sau daya a rana da kowane irin nau’in abin sha. Za a rabu da Basir kowane iri ne da izinin Allah.
‘Ya’yan Dorawa (Kalwa):
1-Maganin Cutar Kansa: Garin ‘ya’yan Dorawa, na maganin kansa kowace iri, idan ana shan sa da Nono.
2-Maganin Makoko: Ana soya ‘ya’yan Dorawa a mayar da su gari, sai a rika sha a ruwan dumi, yana maganin Makoko kwarai da gaske.
Kaucin Dorawa:
1-Maganin Taifot: Ana dafa Kaucin Dorawa a sha karamin kofi sau daya a rana, yana maganin Taifot komai yawansa a jikin mutum.
2-Ciwon Gabobi: Mai fama da ciwon gabobi, ya dafa Kaucin Dorawa ya rika sha, zai sami lafiya da yardarm Allah.
Furen Dorawa:
1-Maganin Ciwon Koda: A dafa Furen Dorawa a sha karamin kofi na ruwa tsawon mako uku, yana maganin ciwon Koda yadda ya kamata.
2- Kumburi Ko Amai: A dake Furen Dorawa ya zama gari, sai a sha karamin cokali a kowane irin abin sha sau biyu a rana, tsawon kwana bakwai, duk yadda matsalar kumburi ta kai za a samu lafiya da yardar Allah.
Garin Dorawa:
1-Maganin Ciwon Ulsa: Garin Dorawa, yana maganin ciwon Ulsa kwarai da gaske. Sai a samu Zuma mai kyau sosai, a zuba a cikin Zumar a rika lasa.













