Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa Muhammed Okitoto, ya yi wa mahalarta taron,da aka yi a dakin taro na NAF Conference Centre Abuja jawabin barka da zuwa.
Ya ce su alluran rigakafi da basu da nasaba da cutar Polio wani tsari ne daga sashen da yake kula da al’amuran da suka shafi Bakondauro da dai sauran wadansu cututtuka, na daga cikin ayyukan da ake yi, shi tsarin yana da matukar muhimmanci ga ita hukumar, domin manema labarai sune wadanda suke sada su da al’ummar da take yin ayyukan saboda su.
Ya ci gaba da bayanin cewa duk wadansu ayyukan da ake yi a hukumar ana yin su ne saboda al’ummar Nijeriya, da suka kunshi manya da kananan yara.Don haka yana da kyau su manema labarai su fahimci al’amarin da ake magana kan sa, wato abinda ita hukumar take bukata domin idan za su sanar da al’umma su fada masu gaskiyar yadda al’amarin ya ke.
An shirya shi ne saboda Editoci da sauran marubuta labaran da suka shafi kiwon lafiya.Ya kara da cewa akwai abubuwan da yawa wadanda za ayi musamman ma alluran rigakafin da basu da nasaba da cutar Polio, don haka ake bukatar hadin kan su manema labarai.
Njideka Oshioke ita ta yi karin haske kan dalilin da yasa aka kira taron inda ta ce daga karshen taron wayar da kan manema labarai ana sa ran,za su san wuraren da za a yi su alluran rigakafin da basu nasaba da cutar Polio.
Bugu da kari kuma a san shi matakin da hukumar ta dauka kan allurar rigakafi na cutar Korona. Akwai tabbacin da ake da shi na sa ran,su mahalarta taron za su san dalilan da suka sa aka kira taron dangane da alluran da basu alaka da Polio.
Ita kuma Dokta Maimuna Hamisu ta yi jawabin ta ne kan alluran da hukumar lafiya matakin farko ta kasa tayi shirin aiwatarwa a 2021 amma ba a samu damar yin su ba kamar yadda yakamata ba, shi yasa ahar abin ya fado zuwa 2022.an yi shirin yi ma yara allurar rigakafin da ba ta da nasaba da cutar Polio,wani karamin sashe ne dake karkashin sashen kawar da cututtuka shi ne ya shirya yin alluran.
Babbar manufar sashen ne ya shirya da kuma aiwatar da alluran rigakafi wadanda bata shafi Polio ba,a cikin kasa Nijeriya da kuma wasu bangarori nata.
Da akwai kuma kai taimakon gaggawa wanda ya shafi barkewar wata cuta,a ko wanne bangare na kasa abin ya faru, wannan kuma yana daidai da ayyukan shi sashen, an yin alluran rigakafin cututtukan da za a iya maganinsu,wato kamar Kyanda,Shawara,Sankarau,da kuma sauran cututtukan da allurar rigakafi zata iya maganinsu.
Ta yi a bayanai kan yadda cututtakan su ke alal misali cutar Kyanda wadda take addabar kananan yara masu shekara biyar, da duk yadda ake kamuwa da su.Har ma lokacin da ake kamuwa da su,lokacin da ake wadannan alluran shi ne a watanni hudu na karshen shekara kamar yadda ta jaddada.
Manufar domin daga watan Satumba zuwa Disamba wannan lokacin ne ya fi dacewa a bada gudunmawa, domin cututtukan basu yaduwa a irin yanayin.Jihohi ashirin da biyar da suka hada da babban birnin tarayya na iya kamuwa da cutar Sankarau.An dauki matakan da suka kamata ta hanyar yin alluran har sau hudu, an yi ma masu shekaru daban- daban da aka yi ma yaran da ba samu damar yi masu alluran rigakafin ba, da aka yi a baya.Inda kuma tace tun daga wancan lokacin kuma ba a kara samun wani labarai barkewar cutar ta Sankarau ba.
Ba kuma kamar yadda aka saba ba a shekarun baya wannan karo Jihohi ma za su bada ta su gudunmawar ta kudi,domin aiwatar da shi tsarin na alluran rigakafi na cututtukan da basu nasaba da Polio.Yaran da za ayi ma allurar rigakafin Sankarau wannan shekarar su ne wadanda ba a samu damar yi masu bane tsakanin shekarun 2011 da 201,wannan kuma yaran da za ayi mawa sune wadanda ba a haifa ba tsakanin shekarun. Har ila yau, ta ce Nijeriya tare da hadin kan hukumar lafiya ta duniya sun kaddamar da wani shiri na kawo dauki kan maganin cutar Shawara,a shekarar 2018, kudurin da ake da shi shi ne a gama da cutar Shawara nan da shekara ta 2026.
Daga karshe manema labara ko ‘yanjarida an yi kira da su cewa duk wani labarin da suka samu, ba sai sun yi gaggawar buga shi ba a Jarida,ko amfani da shi a gidajen Rediyo da Talbijin.Babban abinda ya dace su yi shi ne suke yin bincike don gane gaskiyar al’amarin kafin su kai ga bugawa, musamman ma kamar al’amarin daya shafi kiwon lafiya.
Shi Komai gaskiya da gaskiya labarin kiwon lafiya ne ake bukata, ba wata kumbiya- kumbiya,hukumar lafiya matakin farko ta kasa tana aiki kafada kafada da kafofin yada labarai, saboda ta hanyar ce suke sanar da al’umma halin da ake ciki dangane da al’amarin kiwon lafiya.