Mutane da dama ne suka bayyana alhinin su bayan da shahararriyar ‘uar wasan Tennis ta duniya, Serena Williams ta sanar da yin murabus daga ci gaba da buga wasan bayan shafe shekara da shekaru tana fafatawa tare da lashe kofuna da yawa.
Bisa nasarorin da ta samu a kwallon Tennis, ana kallon Serena Williams a matsayin fitacciyar ‘yar wasa bayan da ta bayyana yin ritaya bayan gasar US Open ta bana, kamar yadda ta rubuta a wani sakon bankwana a Mujallar Bogue cikin farkon watan nan cewa tana janyewa daga wasanni.
- Saudiyya Ta Ja Kunnen Netflix Kan Yada Fina-Finan Da Suka Keta Dokokin Musulunci
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
Nasarorin da Williams ta samu na lashe gasar Grand Slam sau 23, makonni 319 a matsayin zakara a duniya da karin wasu kambu 14 sun karfafa matsayinta a matsayin jarumar da ta sauya fuskar wasan mata.
Williams ba ta taba wucewa zagaye na hudu ba a gasar Grand Slam kafin lashe wasan a shekarar 1999 sai dai da alama an dauki lokaci tun da aka bayyana lashe gasar Grand Slam da Williams ta yi a matsayin abin mamaki, amma bai kasance ba tun bayan da ta lashe gasar tana ‘yar shekara 17 a gasar US Open ta 1999.
Iri na bakwai ya nuna ba wai kawai ya nuna gwanintarta ba ta doke Kim Clijsters, Conchita Martinez da Monica Seles, amma kuma zuciya da mai da hankali a cikin nasara uku a jere bayan koma-baya.
Duk da cewa Serena Williams ta samu nasarori da dama fiye da wasu ‘yan wasa, sai dai akwai wani abu daya da ta rasa ,shi ne kyauta a gasar Olympic kuma wannan abu ne da ya sanya Williams mai shekara 30 jajircewa, wacce kuma ta kwashe tsawon shekarar 2011 tana murmurewa daga wani rauni a kafarta.
Ta kasance cikin ganiyarta inda ta doke Sharapoba da ci 6-0 da 6-1 da yin murna ta hanyar taka wata rawa mai kayatarwa.
Williams ta sake samun nasarar ne shekara 12 bayan samun ta farko, sai dai ta gamu da rashin nasara a shekarar bayan doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar US Open sai dai wani abin burgewa da Serena shi ne farfadowa bayan doke ta.
Bayan wasu kurakure a gasar Wimbledon a 2014 da ta yi, wadda kuma ya janyo hankali kanta inda daga baya aka ce tana fama da mura, inda ta koma kan ganiyarta har ma da lashe gasar US Open watanni biyu da suka gabata a lokacin.
Ta samu nasarar ne da ci 6-4 da kuma 6-4 kan ‘yar kasar Sifaniya Garbine Muguruza inda nasarar ta kasance kyauta ta 21 da ta samu a wasa mai mutum daya-daya bayan haka, Serena ta ci gaba da samun nasarori da dama a rayuwarta.
‘Ya’yan na Williams sun fafata da junansu sau 31, inda Serena ta ke kan gaba da nasara sau 19 -12 kuma bayan kamo tarihin Steffi Graf na samun nasarar Wimbledon sau 22 a shekarar 2016, abin da aka yi ta jira shi ne ko Serena za ta iya shan gaban ‘yar kasar ta Jamus.
Hakan bai samu ba lokacin da Karolina Pliskoba ta doke ta a wasan kusa da karshe na gasar US Open amma ta yi amfani da damar da ta samu a gaba a gasar Australian Open, inda ta samu nasara kan ‘yar uwarta Benus da kuma karya tarihin da Graf ta kafa.
Bayan jinkirta komawa buga wasa a watan Janairu, William ta koma da fara wasa a Indian Wells kuma watanni biyar bayan haihuwar ‘yarta Olympia a Satumbar 2017, William ta bayyana cewa ta kusa rasa ranta lokacin da jini ya yanke mata bayan haihuwa ta hanyar tiyata.
William ta jajirce wajen ganin ta farfado da kuma komawa fagen wasa a shekarar 2018 inda ta fara fafatawa a Indian Wells bayan komawa buga tennis – inda ta yi rashin nasara a hannun Benus shekara 17 daga wani lamari da ya sanya su kauracewa wasa – inda daga baya suka fafata a wasan karshe na Wimbledon da US Open a shekarar.
Duk da cewa Williams ta yi rashin nasara a dukka wasannin, amma ta koma fagen daga da kuma nuna cewa har yanzu tana daya daga cikin taurarin tennis a duniya.
Ta hanyar daga hannunta a sama da sauko da kanta da kuma yin ihu, Williams ta kara nanata abin da muka sani na cewa za ta ci gaba da jajircewa a wasannin tennis sannan murnar da Serena ta yi bayan doke Jessica Pegula a gasar Auckland Classic ya kasance na daban a wajenta kuma nasarar ta kasance ta farko da ta samu a matsayin ta na uwa. Hakan kuma yana nufin cewa William mai shekara 38 ta kasance ‘yar wasa ta farko da ta lashe gasar WTA na mutum daya-daya sau hudu a cikin shekaru 40.
Sai kuma ta yi nasara kan Lindsay Dabenport da Martina Hingis – da aka ayyana su na biyu da na farko a duniya – inda ta rike lambar yabon da ta dade tana burin samu tun lokacin da take karamar ‘yar wasa.
Williams ba ta koma yin wasa a Indian Wells ba bayan abin da ya faru a 2001, sannan a shekarar da ta gabata ta bayyana a matsayin tashin hankali saboda fuskantar takaici bayan janyewa daga matakin wasan dab da na karshe da Benus Williams ta yi saboda raunin da ta ji a karawarta da ‘yar uwarta a wasan karshe da Kim Clijsters daga Belgium.
Ya haifar da wani yanayi mara dadi a tarihin kwallon Tennis inda Benus da Serena da mahaifinsu Richard suka kai kara cewa ‘yan kallo na nuna musu wariyar launin fata saboda an yi ta yi wa Williams wacce ke shekara 19 a lokacin da ‘yan uwanta ihu bayan sun isa kotu, duk da cewa ta yi nasara sau biyu a jerem sannan irin kokari da tayi na doke babbar wanda suka buga wasan abu ne na jinjinawa.
Nasarar da Serena ta yi a kan Benus a wasan karshe na Wimbledon a shekarar 2002, shi ne na 19 a jere, wadda hakan ya sanya ta samu nasara sau 36 da kuma doke ta sau 3, lokacin da Serena ta fara wasa, ta saka a ranta cewa za afi sanin ta a matsayin kanwar Benus.
Sai dai mahaifinta Richard, ya yi hasashen cewa karama daga cikin ‘ya’yan nasa za ta fi zama zakakura, inda hasashen nasa kuma ya zama gaskiya lokacin da Serena ta fara lashe gasar Wimbledon har sau bakwai.
Bayan doke ‘yar uwarta Benus a gasar French Open, Serena ta cire duk wani shakku da ake da ita cewa ba za ta iya fafatawa da ‘yayarta ba a wasan tennis kuma daga baya, Serana mai shekara 20 ta zo ta zarce yayar ta Benus inda ta zamanto ta daya a duniya, mataki kuma da ta rike har na watanni 11 inda ta kasance ta uku bayan Steffi Graf da kuma Martina Nabratiloba, wadanda suka rike matakin na tsawon shekara shida.
Mata shida ne kawai suka taba samun nasarar dukkan kyaututtuka hudu a lokaci guda, inda Serena mai shekara 21 ta shiga jerin sunayen matan bayan samun nasara a kan yayarta a Melbourne.
Williams ta samu nasarori da dama – inda ta lashe gasar Australian Open a 2003 bayan lashe ta French Open da Wimbledon da kuma US Open a 2002 abu kuma da ya sa aka mata lakabi da ‘Serena Slam, sannan a yayin wani jawabi, Serena ta kasa boye farin cikin ta, inda ta ce bata taba tsammanin hakan ba.
Shekarun 2000, sun zamanto masu wahala cike kuma da kalubale a rayuwar William saboda lokaci ne da aka kashe babbar yayarta Yetunde Price a wani harin bindiga, da kuma ya kasance lokaci da take fama da raunuka.
Serena ta yi kasa da mutum 100 da suka fi shahara a duniya a 2006, inda ta koma Melbourne a matsayin ta 81 a duniya.
An yi ta magana kan yadda Serana ta kasance da kuma rashin yin shiri a kan lokaci, sai dai ta bai wa mutane mamaki inda ta zake har zuwa wasan karshe tare da samun nasara kuma lokacin, William ta doke wacce ake kyautata zaton cewa za ta zama ta daya a duniya, Maria Sharapoba inda ta samu nasara da ci 6-1 da 6-2 cikin wasa mai sa’a daya da minti uku.
Williams ta samu nasarar ne na mutum daya-daya bayan doke Maria Sharapoba a wasan karshe, sannan ta samu nasara a wasan da aka buga na mutum biyu-biyu tare da ‘yar uwarta Benus Williams.