Ministan Albarkatun Ruwa, Alhaji Suleiman Adamu, ya yi kira da a rufe Gadar Sarkin Kogi da ke Tiga a karamar Hukumar Bebeji a Jihar Kano domin kiyaye lafiyar masu ababen hawa da masu tafiya a kasa.
Adamu ya yi wannan kiran ne a yayin ziyarar aikin kula da madatsar ruwa ta Dam din Tiga da Bagauda tare da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamna, Hassan Fagge ya fitar a ranar Laraba a Kano.
Ministan ya bayyana cewa madatsun ruwan biyu na aiki yadda ya kamata sabanin jita-jitar da ake yadawa.
Ya umurci hukumar kula da rafin Hadejia-Jama’are da ta ci gaba da kula da sauyin ruwan na yau da kullum.
Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, ya bada tabbacin aniyar gwamnati na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp