Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, ya ce ya bai wa matasa marasa aikin yi 1,000 tallafin Naira miliyan 100 a garin Biu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai, Baba-Sheik Haruna, ya sanyawa hannu kuma ya fitar a Abuja ranar Juma’a.
- Kotu Ta Soke Takarar Dare A Matsayin Wanda Zai Yi Wa PDP Takarar Gwamna A Zamfara
- Tagomashin Da CBN Ya Samar Wajen Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Sana’o’i
Ya ce tallafin, wanda aka gudanar a Kadafur da ke garin Biu, za a yi amfani da shi ne a matsayin jarin fara kasuwanci ga masu kananan sana’o’i domin bunkasa tattalin arzikin yankin.
Taron dai wani bangare ne na rangadin kwanaki uku da gwamnan ya kai hedikwatar Sanatan Borno ta Kudu, domin kaddamar da ayyuka daban-daban da gwamnatinsa ta aiwatar.
A yayin da yake kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da wannan tallafin da idon basira, gwamnan ya ce gwamnati za ta ci gaba da kokarin rage zaman kashe wando da yaki da fatara ta hanyar taimaka wa marasa galihu da dai sauransu.
Ya bayyana cewa talauci, rashin aikin yi da rashin ilimi ne suka taka muhimmiyar rawa wajen bullar Boko Haram a jihar.
A tsawon wannan lokaci, Zulum ya kaddamar da Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mega da ke Buratai mai daukar dalibai 1,500, sannan ya bude babbar makarantar Islamiyya ga dalibai 1,200 da ke Biu da kuma Sashen Sa ido da tantance Ilimi na Shiyya a garin Biu.
Tun da farko kwamishinan matasa, ci gaban wasanni da yaki da fatara, Saina Buba, ya ce an zabo wadanda suka amfana su 1,000 ne daga gundumomi a fadin karamar hukumar Biu.
Ya ce gwamnan, wanda tun a shekarar 2019, ya kaddamar da wasu tsare-tsare na tattalin arziki da ke bayar da tallafin kudi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, bai bar masu nakasa da kuma tsofaffi ba.