Sheikh Dr Yusuf Ali, ya bayyana cewar yin aiki da Dokokin Allah su ne kawai mafitar da za su kawo karshen matsalolin da suke addabar kasar nan ta Nijeriya.
Ali wadda shine Sarkin Malaman masarautar Gaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira ta musamman da ‘yan jarida akan karramawar da Gidauniyar ‘Ganduje Foundation’ ta yi masa kan hidimar da ya ke yi wajen isar da sakon Allah (SAW) a ranar Juma’a a zawiyyarsa dake Unguwar Tudun Maliki a cikin birnin Kano inda ya samu halartar’ ‘yan jaridu da kuma wasu muridan Shehin Malamin.
An karrama Shehin Malamin ne a yayin rufe musabakar Alkur’ani da Gidauniyar Ganduje take shiryawa a kowacce shekara.
Shehin Malamin ya jaddada cewa: “Babu wata madogara yanzu a dukkanin al’ummar duniya baki daya, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba illa wannan addinin, da kuma wannan littafin (Kur’ani). Duk wadansu tsare-tsare da wadansu bincike-bincike da duk wani abu da za a gwada, an gwada, amma duniyar nan ga halin da ake ciki, haka take, sama da kasa, a birkice, ba a samu yadda ake so ba.
“Saboda haka babu wani wata fata ga al’ummar yanzu da wadanda za su zo nan gaba illa wannan addini da kuma wannan littafi,” ya tabbatar.
Ya kara da cewa, “Duk wani bincike da aka yi a duniyar nan, komai zurfinsa, duk mamakinsa, duk sararin samaniyyar da aka tafi, duk kasar da aka tafi, duk abin da aka kirkiro, za ka samu Alkur’ani ya yi bayaninsa dalla-dalla. A bakin wa aka ji? A bakin Manzo Allah (SAW),” ya nusasshe.
Ya lurantar da cewa ka da kawai a tsaya a karanta Alkur’ani, a ci gaba da zurfafa bincike, Alkur’anin zai warware dukkannin matsalolinmu baki daya.
“Mu yi koyi da shi kamar yadda dabi’un Manzon Allah (SAW) da halayyarsa ya kasance Alkur’anin ne. Duk abin da Alkur’ani ya hana, ya hanu, duk abin da Alkur’ani ya ce ya yi shi ne yake yi. Ba abin da Alkur’ani ya bari.
“Duk abin da za mu yi ya kasance Kur’ani shi ne zai kasance ya zama jagoranmu. Abin da ya ce mu yi shi ne za mu yi. Za a ga abubuwa sun rincabe baki daya. Saboda mene? Saboda wanda ya halicce mu ya ce ga abin da za a yi a cikin littafinsa na karshe, bamu yi.
“Annabin da ya aiko na karshe babu wani Annabin bayanshi. Mune al’ummar karshe. Amma kuma ba ma bin abin da ya ce. Mu koma wannan littafi ga baki daya, ya zama shi ne zai zame mana mizani a shugabancinmu, a mulkinmu, a sana’armu, a nomannu, a aurenmu, a tarbiyyarmu, a huldarmu da jama’a. Abin da ya shafi lafiyarmu, da abin da ya shafi duk wani hali na siyarmu da sauran su.”
Sheikh Yusuf Ali ya kara da cewa, makasudin ba shi wannan lambar girmama shi ne; saboda hidimar da yake gudanarwa shekara da shekaru wajen daukaka addinin Musulunci tare da zaburarwa da karfafawa kan karatun Alkur’ani mai girma.
Shehin Malamin ya ce yana godiya ga Allah ta’ala bisa shiriyar da shi da ya yi da littafin Alkur’ani mai girma.
Shaikh Dr Yusuf Ali har, ya cigaba da cewa, ba yau ne farkon ba shi kyauta da Gwamna Ganduje ya yi masa ba. Amma ya ce wannan ta sha bamban saboda an ba shi ne kan Alkur’ani.
Ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wannan karammawar.
Sai ya yi kira ga sauran gwamnoni da shugabanni a matakai daban-daban da su bunkasa addinin Musulunci da karfafawa masu kokarin haddace Alkur’ani guiwa.
Gidauniyar ta Ganduje ta kasance tana ilmantarwa da karfafawa mutane karatun Alkur’ani, da gina makarantu da masallatai tare da musuluntar da wadanda ba Musulmi ba.