Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), ta yi gargadin cewa duniya na tunkarar wani yanayi na matsin tattalin arziki sakamakon rikice-rikice da dama, wanda ke nuna bukatar da ake da ita samar da sabbin tsare-tsare da za su habaka tattalin arziki.
Darakta-Janar ta WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa batutuwa masu alaka da yakin Rasha da Ukraine da kuma dumamar yanayi sun yi taron dangi wajen assasa tsadar kayayyaki musamman na abinci baya ga haddasa karancin makamashi a sassan duniya, dai-dai lokacin da ake shirin fita daga matsalar da annobar cutar Korona ta jefa duniya.
- Buhari Ya Haramta Siyan Makamai Ga Jami’an Tsaron Sa-Kai A Jihohi
- Amurka Ta Yi Kaurin Suna Wajen Kakaba Takunkumai
A jawabinta a wajen taron kasuwanci da zuba jari na shekara-shekara da ke gudana a Geneva, shugabar ta WTO ta ce wajibi ne a samar da sabbin dabarun habaka tattalin arziki da za su ragewa duniya radadin halin da ake ciki da kuma barazanar da ke tunkarowa.
A cewarta ana cikin wani yanayi da kiri-kiri ake iya hango barazanar da tattalin arziki ke tunkara wanda don haka dole a yi aiki tukuru wajen laluben hanyoyin murmurewa tun gabanin fadawa a matsalar baki daya, ta yadda za a dauki matakan rage tasirin da illar ta mashassharar tattalin arziki za ta yi wa Duniya.
Ngozi Okonjo-Iweala ta kafa hujja da yadda dukkanin hasashen tattalin arzikin da Bankin Duniya da kuma asusun bada lamuni na Duniya suka yi ke nuna mummunar koma bayan da ke tunkaro Duniya.
Darakta-Janar din, ta ce kasashe a yanzu na fama da matsalolin rashin tsaro, dumamar yanayi, tsadar kayan abinci da kuma tsadar makamashi wanda dukkaninsu a lokaci guda, wanda kai tsaye zai iya ruguza kasashe da dama.