Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Litinin cewa, Amurka ta yi kaurin suna wajen kakaba takunkumai.
Ya ce bisa alkaluman kiddidga, takunkuman Amurka sun karu da kaso 933 daga shekarar 2000 zuwa 2021. Yana mai cewa, kawo yanzu, Amurka ta kakaba takunkuman tattalin arziki kan kasashe kusan 40 a fadin duniya, lamarin da ya shafi kusan rabin al’ummar duniya tare da haifar da matsalolin jin kai masu tsanani.
Ya ce gwamnatin Amurka da ta gabata, ta kakaba takunkumai sama da 3,900 ko kuma takunkumai sau 3 a kowace rana a matsakaicin mataki.
Kafafen watsa labaran Amurka sun bayyana cewa, Amurka ta dauki takunkumai a matsayin makamin da ta fi so a cikin manufofinta na harkokin waje. (Fa’iza Mustapha)