A yayin wata ziyarar da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefele ya kai lokacin bikin baje kolin kasuwar duniya da ke jihar Kaduna da kuma wata ziyara da ya kai a wasu gonakin da ke fadin Nijeriya a watannin baya, ya yi amfani da lokutan ziyarar don sake saita wasu daga cikin tsare-tsaren da fito da su.
Ya yi hakan ne, saboda yadda tsare-tsaren da aka samar a baya, aka gaza cim ma nasara a kansu, musamman wajen zuba kudi a fannin kanana a matsakaitan sana’o’i hannu da kuma a fannin aikin noma.
- Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Canada Da Austriliya Da Su Duba Matsalarsu Ta Nuna Wariya Ga ‘Yan Asalin Wurin
- Shirin Twitter Space Na LEADERSHIP Hausa: Yadda ‘Yan Nijeriya Za Su Kauce Wa Komawa ‘Yar Gidan Jiya A Zaben 2023
Akasarin masu bibiyar tsaretsaren na Godwin, na da yakinin cewa, kwalliya za ta biya kudin sabulu wadanda kuma idan ya kammala wa’adin shugabancin CBN zai ci gaba da tuna Godwin haka ya bar dimbin tarihi.
Godwin a ziyarar da ya kai a gonakan da ke a jihar Edo, gonakan sun amfana da daukin da Godwin ya samar a gare su ta hanyar zuba kudade, musamman don a ceto tattalin arzikin Nijeriya da kuma kara bunkasa fannin aikin noma a kasar.
A kasuwar duniyar ta Kaduna, Godwin ya yi amfani da damar, inda ya sanar da ‘yan Nijeriya cewa, CBN ya raba Naira biliyan 948 ga manoma, inda fannin kanana da matsakaitan sana’o’i ya samu naira biliyan 368.79 duk a cikin shekaru shida da suka wuce.
A bisa fashin baki a kan wannan adadin, jimlar masu gudanar da kanana da mataitan sana’o’i guda 4,478,381 ne suka amfana, inda manoma suka samu bashin naira biliyan 948 saga gun Babban Bankin Nijeriya CBN domin noma kadada miliyan 5.2 a daukacin fadin kasar nan tare da nufin samar da ayyukan yi na kai tsaye da kuma wanada ba na kai tsaye ba guda 12.5.
Bugu da kari, Babban Bankin na CBN ya kuma rabar da bashin Naira biliyan 368.79 ga sama da masu yin kananan sana’o’i guda 648,052 suka amfana, sai kuma masu yin matsakaita da kananan sana’o’i, kimanin guda 130,000 suka amfana.
Kwararru masu yin fashin baki a kan fannin aikin noma da ke bibiyar yadda fannin ke tafiya daga watan Nuwanbar shekarar 2015, shirin aikin noma na Anchor Borrowers na Gwamnatin Tarayya da CBN ke tafiyar da shi, ya taimaka matuka wajen wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, musamman wajen kara habaka noman a tsakanin kananan manoma a kasar nan.
Ya na da kyau a sani cewa, kirkiro da tsare-tsaren da ban da ban, anyi hakan ne domin sake dora fannin akan tsarin da ya dace, inda a zahirance, kananan manoma da dama sun amfana, inda hakan ya kuma kara taimaka wa wajen habaka tattalin arzikin Nijeriya.
A karon farko na kama aiki a matsayin Gwamnan CBN, Godwin ya kasance ya na da kudurin habaka tattalin arzikin kasar tarer da kuma samar da alakiblar mai dorewa don bunkasa tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar yin amfani da tsare-tsare kamar kirkiro da shirin (YEDP) da zai bunkasa kasuwancin matasa da habaka fitar da kaya daga Nijeriya zuwa ketare (ESF); kirkiro da shirin (AGSMEIS), na zuba jari kan matsakaitan Da kananan sana’oi na yin noma don riba kirkie da shirin (PAS) na noman shinkafa ‘yar gida da kuma kirkiro da shirin (AADS) wanda zai kara habaka samun kudin shiga ga kananan manoma.
Har ila yau, Godwin ya kirkiro da tsarin (TIES) wanda CBN je zuba kudade don a Horar da daliban da suka kammala Jami’a a kasar.
Ya kuma kirkiro da tsarin (PPP) wanda manufarsa ita ce, a sarrafa kaya ingantatu da za su dace daidai da tattalin arzikin kasar, musamman don kasar ta daina dogaro akan shigo da kaya saga ketare.
Har ila yau, kimanin naira biliyan 3.20 aka rabawa wadanda suka amfana su 28 a kashi na farko, inda a fannin kerere suka samu 14 suka amfana sai kuma a fannin aikin noma 12 suka amfana sai kuma fannin kiwon lafiya ya amfana da biyu.
Bugu da kari, yin amfani da shirye-shiyen da Godwin ya kirkiro kamar na'(NIRSAL); (NEMSF); (RSSF); ds samar da Cibiyoyin (EDCs) sun taimaka matuka wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Wanzar da wadanda nan tsare-tsaren a aikace, ya taimaka matuka wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya,musamman ganin yadda, fannin aikin noma ya samu karbuwa a gun jama’a, inda suka dauki fannin ba wai kawai su noma abinda za su ci ba, har da gudanar da yin noma domin samun riba, samar da ayyukan yi.
Kafin zuwan tsare-tsaren na Godwin, a baya ana kashe kusan naira tiriliyan daya ne wajen shigo da kaya daga ketare zuwa cikin kasar nan.
Har ila yau, daukin da Godwin ya samar ta ingantacciyar hanyar bayar da daukin kudade ya taima wkjen kara habaka fannin aikin noma a kasar da kuma kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Bisa wasu alkaluman da aka hukumar kididdiga da hukumar NBS ta kasa ta fitar ta nuna cewa, gudunmawar da fannin aikin noma na kasar ya bayar ga tattalin arzikin Nijeriya ya karu zuwa kashi 22.35 a cikin dari a zango na daya daga kashi daga 19.79 a cikin dari. kamar yadda yake a 2015.
Babban mahimci shi ne karin da aka samu kashi 2.2 a cikin dari a fannin aikin noma a shekarar 2020, a lolacin da tattalin arzikin kasar ya samu kashi 1.92 a cikin dari.
Karin wata nasarar ita ce, ta kashi 3.4 a cikin dari da fannin ya samar, a zango na hudu na shekarar 2020, wanda kuma ya kasance shine mafi karuwarsa aka samu tun daga shekarar 2017.
Gilbert mazauni na zaune a Abuja kuma mai yin fashin baki a fannin tattalin arziki.