Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da gamayyar kungiyoyin farar hula sun jaddada bukatar gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci, inda suka ce dole ne al’umma su zabi cancanta a zaben 2023 mai zuwa.
Sarkin ya ce ‘yan Nijeriya sun cancanci su samu sauyi mai kyau a kasar, inda jaddada bukatar zaben shugabannin da za su iya tsayawa don yi abin da ya dace.
- Da Dumi-Dumi: Ibrahim Gusau Ya Zama Sabon Shugaban Hukumar Kwallon Kafa Ta Nijeriya
- Bana An Noma Masara Da Tsadar Gaske – Makarfi
“Don haka, ina ganin muna bukatar yin abubuwa da yawa tun daga sama har kasa saboda yawan ‘yan Nijeriya a kasa, su ne masu yanke abin da zai wakana. Kuma jama’a za su iya amfani da kuri’unsu su zo su zabi shugabanni nagari,”
Bayero wanda Ma’ajin Kano, Lamido Umar Yola ya wakilta, a wajen wani taron da kungiyoyin fararen hular suka shirya a Abuja, domin tunkarar zaben 2023.
Shugabar kungiyar ta kasa, Elizabeth Oziri, yayin da take jawabi ga ‘yan jarida ta ce: “Mun samu isassun hanyoyi da dama. Amma Muna son a bai wa mutane damarsu.”
Oziri ta jaddada bukatar jama’a su yanke hukuncin wanda zai jagorance su a shekarar 2023, ta kuma kara da cewa ya kamata jama’a su yi taka-tsantsan kan waye ya kamata su zama shugabanninsu.
Ta ce kungiyar na da burin ganin Nijeriya ta samu daidaito ta fuskar shugabancin kasar.
Oziri ta kuma ce kungiyar na da nufin tabbatar da an ji muryoyin jama’a.
Ta ce, “Ya kamata su yi bincike game da tarihin wadannan shugabannin. Su je su duba su tabbatar da ingancinsu.
Oziri ta bayyana cewa, a yayin da kasar nan ke kara kusantar zabuka, kungiyoyin farar hula za su taka rawar gani ta hanyar fadakarwa, wayar da kan al’umma game da ‘yancinsu na kada kuri’a, da hada kai da gwamnati wajen sanya ido a lokutan zabukan.
“Kungiyoyin farar hula za su iya tattaunawa da gwamnati, su yi hadin gwiwa da su kan abubuwan da jama’a ke bukata daga gare su,” in ji Oziri.