Kasar Sin za ta samar da kyakkyawan yanayi da hidimomi masu inganci ga bakin dake aiki a kasar tare da bayar da karin tallafi ga aikinsu na bincike da kirkire-kirkire.
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ne ya bayyana haka a babban dakin taron al’umma dake Beijing, a lokacin da yake ganawa da baki ma’aikata da suka samu lambar yabo ta abota ta shekarar 2022, wadda gwamnatin Sin kan bayar a kowace shekara, domin girmama fitattun baki ma’aikata a kasar Sin.
Firaministan ya kara da cewa, Sin ce babbar kasa mai tasowa a duniya, kuma aikin zamantar da kasar yana da wahala da nisan zango. Ya ce ba tare da la’akari da sauye-sauyen da za a samu a duniya ba, kasar Sin za ta ci gaba da mayar da hankali kan gudanar da harkokinta yadda ya kamata da tabbatar da samar da kyakkyawar rayuwa ga dukkan Sinawa.
Da yake bayyana cewa ci gaban da Sin ta samu cikin sauri yana da alaka da manufarta ta yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, ya ce kasar za ta ci gaba da zurfafa gyare-gyare da kara bude kofa, da ingiza kuzari mai karfi ga ayyukan ci gaba.
Bugu da kari, ya bayyana baki ma’aikata a matsayin jakadun abota da gada mai muhimmanci tsakanin Sin da duniya, yana mai cewa, Sin na maraba da baki su shiga cikin aikin zamantar da kasar ta hanyoyi daban daban. (Fa’iza Mustapha)