Masu ruwa da tsakani a fannin noman shinkafa don riba a jihar Taraba,da Jigawa da Kano da Binuwai da Neja da Kogi da Kebbi da sauran wasu jihohin, na cikin tsaka-maiwuya, sakamakon ambaliyar ruwan sama, inda suka sanar da cewa, annobar ta sa ba za su samu amfani mai yawa ba.
Annobar ta kutsa cikin gonakinsu na shinkafar, inda hakan ya jawo musu asara.
- Mutum 108 Ne Suka Mutu Sakamakon Ambaliyar A Jihar Jigawa
- Turmutsutsu Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 174 A Filin Ƙwallo A Indonesia
Rahotanni sun ce, iftila’in ya samu gonakinsu na shinkafar, a yayin da take kan girma.
Akasari dai, a wasu jihohin an fi samun yawan ruwan sama mai yawa daga watan Satumba.
Shinkafa dai ta kasance akasarin cimar al’ummar Nijeriya, inda gwamnatin tarayya mai ci ke kokarin baiwa fannin kulawar da ta dace, tun a 2016.
Sai dai, abin takaici, Nijeriya a duk shekara na fuskanyar kalubalen ambaliyar ruwan sama, inda hakan musamman ke shafar gonakan manoman Shinkafa da kuma sauran amsu ruwa da tsaki a kasar.
Hakan ya kawo wasu manoman sun yi asara mai yawa, inda wasu rahotanni daga jihar Taraba sun ce, dubban manoman shinkafa a kananan hukumomi biyar, sun tabka asara saboda ambaliyar da ta ta so daga kogin da ke a jihar Biniwe.
An ruwaito cewa, kusan kashi 90 na gonakin shinkafar, ambaliyar ta lalata, inda ake tunin, hakan zai jawo karancin samun Shinkafar da ake noma wa a bana.
Dubban kadadar da abin ya shinkafar sun kasance ne a Karim-Lamido da Lau da ArdoKola da Gassol da kuma Ibbi.
Wata namomiyar Shinkafar a yankin Mutum biyu da ke a karamar hukumar Gassol Madam Rita John, ta ce, ta ciyo bashin naira 400,000 daga gun wanu dilolin Shinkafar bisa burin za ta samu riba, amma kuma ambailyar, ta yi mata barna a gonarta.
Shi ma wani manominta mai suna Abubakar Dauda, ya sanar da cewa, ya ciwo bashin naira 350,000 ne daga gun wani dilan Shinkafar domin yin noman, amma ambaliyar ta lalata masa gonarsa.
Bugu da kari, manyan manoma sune abin ya fi shafa, ganin cewa, sun zuba miliyoyin naira domin yin nomanta Shi ma wani dan majalisar dokokon jihar Taraba Suleiman Abbas, ya sanar da cewa, ya zuba dimbin kudade a nomanta, amma ambailyar ta lalata masa gonarsa, inda ya sanar da cewa, akwau bukatar gwamnati ta kawo masu dauki.
Haka shi ma Yakuku Adamu, wanda babban manominta ne ya bayyana cewa, a baya yana dibansa sama da buhunhuna 3,000 na Shinkafar cikin gida, amma ambailyar ta lalata masa gonarsa.