An gurfanar da Abidemi Oguntuyi mai shekaru 23 a gaban wata kotun majistare da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo, bisa zarginsa da daba wa wata mata wuka mai suna Abiye mai shekaru 40 a duniya.
Marigayiyar, wadda ke zaman haya a gidan wanda ake zargin, an ce ta yi kokarin sasanta rikicin da ya barke tsakanin Oguntuyi da dan uwansa a lokacin da aka daba mata wuka a wuyanta da wasu sassan jikinta.
- Ambaliyar Ruwa Ta Shanye Titin Abuja Zuwa Lakwaja
- Kungiyoyin Kasa Da Kasa Sun Yi Fatan Gudanar Da Babban Taron Wakilan JKS Karo Na 20 Cikin Nasara Yayin Da Kasar Sin Ke Bikin Ranar Kafuwar Kasa
An gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa laifuka biyu na kisan kai da kuma yunkurin kisan kai.
Lamarin ya faru ne a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, da misalin karfe 11:00 na safe a unguwar Akungba-Ibaka Akoko, karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a jihar.
Laifukan sun ci karo da sashe na 319 da 355 na dokar laifuka ta Jihar Ondo, karkashin sashe na 37 na dokar 2006.
Simon Wada, dan sanda mai shigar da kara, ya bukaci da a tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Olokuta yayin da kotu ke jiran shawarar daraktan kararrakin jama’a, DPP.
Lauyan wanda ake tuhuma, Adeola Kayode, ya yi bukaci a dage shari’ar don ba shi damar shigar da kara a rubuce ga mai gabatar da kara.
Alkalin kotun, D.S. Sekoni, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a hannun ‘yansanda har zuwa lokacin da za a yanke hukunci sannan ya dage shari’ar har zuwa ranar 7 ga Oktoba, 2022, domin yanke hukunci.