Assalam Alaikum. Don Allah me ake nufi da kyakyawan karshe, akwai wasu sifofin da siga na mutuwa da yake nuna cewa in sha Allah mutum ya yi kyakyawan karshe?
Wa alaikum assalam, akwai alamomin da yawa da suke nuna kyakykyawan karshe daga ciki akwai:
- Cikawa da Kalmar Shahada, saboda fadinAnnabi (SAW) “Duk Wanda maganarsa ta karshe ta zama La’ilaha illallahu zai Shiga aljanna”.
- Mutum ya mutu yana aikin alheri kamar sallah Hajji, saboda fadin Annabi SAW ” Ana tashin bawa akan abin da ya mutu yana yi”.
- Idan mutum ya rasu Daren juma’a ko yininta saboda fadin Annabi SAW “Duk Wanda ya rasu Daren juma’a ko yininta Allah zai kare shi daga azabar Kabari”
- Idan mutum ya yi shahada kamar mace ta mutu wajen haihuwa ko ciwon ciki ko nutsewa a ruwa ko ya mutu a ciwon Kwalara ko kare kansa ko dukiyarsa DSS
Idan mutum ya rasu yana gumin goshi kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi.
Allah ne mafi sani.