Daya daga cikin shugabannin al’ummar garin Gwanda da ke karamar hukumar Kuda ta jihar Kaduna, Mai unguwa Yahuza Gwanda, ya bayyana cewa, Allah ya azurta wannan yanki nasu da kasar noma, inda suke noman damina da na rani mai yawan gaske na wasu nau’ukan amfanin gona, lokacin rani da damina.
Yahuza ya ce, yanzu haka tuni har sun fara shirin noman rani, amma sai ya ce, babbar fargabar da suke da ita, ita ce, wani lokacin bayan sun shimfida noman rani, sai rijiyoyin da suke amfani da su wajen ban-ruwa su kafe, wannan kan haifar musu da asara, mai yawa, kuama na karya musu gwiwa.
- Majalisa Ba Ta Da Hurumin Dakatar Da Shugaban Hukumar Zabe Ta Jiha – Shugaban NBA
- Yadda Ake Tabbatar Da Ci Gaba Mai Inganci A Birnin Shanghai Na Kasar Sin
Saboda haka sai yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna da ta tallafa musu ta haka musu dam, wanda zai taimaka musu wajen bunkasa rayuwarsu da dogaro da kansu da kuma wadata kasa da abinci.
Mai unguwa ya ci gaba da cewa, duk da wannan matsala da suke fuskanta ta rashin madatsar ruwa, suna yin noma mai yawan gaske, kuma suna samun alheri daidai gwargwado.
Ya ce, ita karamar hukumar, karamar hukuma ce da al’umma ta ke bai wa noma muhimmanci, wanda kuma hakan ya sa suka yi fice a dukkan fadin kasar nan wajen noman rani da na damuna, saboda haka ya ce, manoman yankin na garin Gwandar ke bukatar kara bunkasa wannan sana’a ta su ta noma, hakan kuma zai kara musu karfin gwiwar yin noman musamman na rani idan gwamnati ta waiwaye su da bukatar da suke da ita.