Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta sallami shugaban masu rajin fafutukar kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu.
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Kanu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume 15 da suka shafi cin amanar kasa da ta’addanci, laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa a yayin yakin neman zabensa.
- An Yi Wa Manoma 5 Yankan Rago A Wani Sabon Rikici A Benuwe
- 2023: Kuri’a Miliyan 95 Ce Za Ta Bayyana Wanda Zai Gaji Buhari – INEC
Wani kwamitin mutane uku da kotun daukaka kara, ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin yi masa shari’a bisa la’akari da yadda aka tsare shi da kuma yadda aka yi da shi wanda ya sabawa ka’ida.
Kotun ta ce tuhume-tuhume 15 da ake tuhumar Kanu ba a bayyana, kwanan wata, lokaci da kuma yanayin laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba kafin a mika shi zuwa Nijeriya, wanda ya sabawa yarjejeniyar kasa da kasa.
Kotun ta ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta kasa bayyana inda aka kama Nnamdi Kanu duk da zarge-zargen da ake yi masa.
An Zarge Shi Da Laifin Cin Amanar Kasa
Mista Kanu ya sha yin kira da a balle wani yanki na kudancin Nijeriya domin kafa Jamhuriyar Biyafara.
A watan Oktoban 2015, hukumomin Nijeriya sun kama shi kan tuhume-tuhume 11 da suka hada da “ta’addanci, cin amanar kasa, jagorantar al’umma ba bisa ka’ida ba, buga labaran batanci, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da shigo da kaya ba bisa ka’ida ba, da sauransu.
“An bayar da belinsa ne a watan Afrilun 2017 saboda dalilai da suka shafi rashin lafiya.
“Sai dai Mista Kanu ya tsere daga kasar a watan Satumban 2017 bayan da sojoji suka mamaye gidansa da ke Afara-Ukwu, kusa da Umuahia a Jihar Abiya.
“Daga nan ne aka gan shi a Isra’ila, daga baya kuma ya ci gaba da tara magoya bayansa a Nijeriya don yin amfani da tashin hankali wajen samun ballewa.
“An zarge shi da laifin yin zagon kasa da ya hada da tada tarzoma ta hanyar talabijin da rediyo da watsa shirye-shirye ta yanar gizo a kan Nijeriya da jihohi da hukumomin Nijeriya,” in ji Ministan Shari’a, Abubakar Malami bayan an sake kama Kanu tare da dawo da shi Nijeriya a watan Yuni 2021.
“An kuma zargi Kanu da haddasa tashin hankali musamman a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin fararen hula, sojoji, jami’an ‘yansanda da lalata cibiyoyin farar hula da hukumomi.”
Mista Kanu ya musanta aikata laifikan da ake tuhumarsa da su.