Kamar kowace shekara, a bana ma al’ummar Musulmai masoya Annabin Tsira, Annabi Muhammad sun fito domin yin zagayen gari domin nuna murna da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW) a cikin garin Bauchi.
Zagayen Maulidin na bana ya kayatar ya kuma samu armashi kana an gudanar da shi lafiya ba tare da wani tashin hankali ko kalubale ba.
Wakilinmu ya labarto cewa tun safiyar ranar Lahadi ne dai al’ummar musulmai, da kungiyoyin addini, gami da mawaka da sassan masoya Annabin suka fito domin yin wannan jerin gwanon da aka saba gudanarwa duk shekara cikin ado, kwalliya, fareti, wakokin yabon Manzo da sauransu.
Kamar yadda aka saba, dandamin filin kwallo na Kobi shine ke zama mikatin Maulidin a duk shekara kuma makarantun Islamiyoyi ne ke fara shiga sawu, inda ake fita bisa layi tare da nizami, haka a bana ma zancen ya gudana, inda masu maulidin suka taso daga Kobi, suka nausa kofar Fadar Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu inda suke mika masa gaisuwar Maulidin yayin da shi kuma ke saman fadarsa zaune na amsar gaisuwar.
Baya ga hakan, masu zagayen sun nausa zuwa titin Santaral, suka nufi titin Kofaran da zarcewa Bakin Kura, zuwa Tashan Babiye kana layin ya wuce zuwa titin Wunti da sauran manyan hanyoyin jihar dukka domin nuna farin ciki da wannan ranar ta Maulidi.
A gefe daya, masu maulidin kan raba kyautuka da alawa da fulawowi ga masu kallonsu, a yayin da su masu kallon ke mika kyautuka ga wadanda suke kan sahun Maulidin. Inda zagayen ke kara dankon kauna da fahimtar juna a tskanin bangarori daban-daban.
Da muke zantawa da daya daga cikin malaman addinin musulunci kuma almajirin Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Malam Muhammadu Sunusi, ya bayyana cewar suna fitowa zagayen Maulidin ne domin nuna kauna da soyayya ga Annabi Muhammad (S), har ma ya ce zagayen na baya ya kayatar sosai.
“Alhamdullahi zagayen baya sai godiya wa Allah domin an samu sauye-sauye da gyare-gyare da suka kara inganta zagayen na bana.
“Muna fitowa zagayen Maulidin nan ne domin Allah domin Annabi (S), ka ga dai da idonka babu wani abun da ake yi da aka daina, maza da mata, yara da kanana, tsoffi kowa ya fito domin nuna murnarsa da zagayowar wannan ranar kuma cikin tsari.
“Kuma abun da ake yi dai shine aka saba, wato raya yabon Manzon Allah (SAW), nuna soyayayarsa da tunawa ma jama’a Manzon nan da yaren labaranci, Hausa ga wasu ma da sifa da shiga irin na Yarbawa da Inyamurai wasu Fulani haka aka kayatar da wunin nan gaba daya tun safe har dare Manzon Allah ake anbato a jihar nan domin duniya ta shaidi mun yi wa Allah godiya a kan wannan ni’ima da ya yi mana.”
Malamin ya ce godiya ne suke yi da ni’imar da Allah ya musu, yana mai cewa babu wata ni’ima da ta kai samun Manzon Allah.
“Don haka muka fito domin nuna godiya da wannan ni’ima, da rahama da aka samu sakamakon zuwan Manzon Allah.”
Sunusi wanda ake wa lakabi da fiya-fiya, ya kuma nuna cewa an yi taron lafiya an kammala lafiya don haka ne suke kara godiya ga Allaha kan hakan, “Masu sukar Maulidi ya kamata zagayen da ake yi ya zama musu wa’azi na cewa ya kamata su daina domin hakan ba ya rage komai sai kara armashi wa Maulidi.”
Muhammadu Sunisi ya yi fatan Allah maimaita kana ya nuna gamsuwarsa da yadda aka yi tsari masu kyau wajen gudanar da maulidin cikin kwanciyar hankali da annashuwa.
Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan zagayen, wakilin ‘yan uwa musulmai Almajiran Sheikh Zakzaky a jihar Bauchi, Malam Ahmad Yusuf Yashi, ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga jama’a da su dauki maulidi a matsayin babban alamin hadin kai da inganta zaman lafiya a tsakanin jama’a.
“Kamar kowace shekara a bana ma ranar 12 ga watan Rabi’u Auwal mun fito ne domin nuna farin ciki da zagayowar ranar haihuwar Manzon Rahma, Muhammadu Dan Abdullahi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi), kuma alhamudullahi ba mu kadai ma al’umma gata nan gabaki daya an fito domin yin musharaka wajen nuna wannan farin cikin.
“Sakona a irin wannan rana shine cewa mu yi amfani da wannan dama wajen dinke baraka a tsakanin al’ummar musulmai, duk da banbance-banbancen da ke akwai, tun da Manzon Allah ya hadamu, Kaaaba ta hadamu mu yi amfani da wannan damar mu zauna mu dinke mu zama abu guda domin cigaban al’ummar musulmai da jama’a gabaki daya,” Inji Yashi.
A sakonsa na fatan alkairi ga masu zagayen Maulidin, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya nuna farin cikinsa kan yadda zagayen na bana ya gudana cikin kwanciyar hankali da armashi, sai ya yi kira kan kara hada kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma domin rayuwa take ingantuwa a jihar.
Ya kuma yi fatan Allah maimaita tare da taya al’umma murnar zagayowar wannan maulidin na 2022.
A sakonsa na ranar Maulidi da gwamnan Bala Muhammad ya fitar, ya taya al’ummar musulmai murnar zagayowar ranar Maulidi tare da rokonsu da su kasance masu koyi da dabi’un Manzo.
A sakon da ya fitar ta hannun kakakinsa, Muktar Gidado, gwamnan ya ce dukkanin rayuwar Manzon Allah abin koyi ne ga al’umma, kuma a cewarsa, Annabi ya koyar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, kyauta, Dabi’u na kwarai, don haka ne ya nemi al’umma da su yi koyi domin kyautata zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya yi fatan cewa jama’a za su yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kasa a yayin da suke gudanar da shagulan bikin Maulidi na bana.
Daga bisani ya yi fatan cewa za a gudanar da taron Maulidin a ciki da wajen jihar lafiya kamar yadda aka fara cikin kwanciyar hankali. Sanann, ya nemi jama’a da su kara yi wa gwamantinsa addu’a domin ta cimma nasarorin da ta sanya a gaba.
Shi kuma Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci jama’a da su yi addu’ar samun shugabanni na kwarai da gudanar da zaben 2023 cikin kwanciyar hankali.
Da yake jawabi a wajen taron Maulidin da ya saba shiryawa na bana, Dahiru ya ce suna gudanar da Maulidin ne domin raya ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW), ya kuma jawo hankalin al’umma da su cigaba da koyi da halayen Manzon Allah a kowani lokaci.
Shi kuma a jawabinsa a wajen taron Maulidin Manzon Allah da Sheikh Dahiru Bauchi ya shirya, gwamnan Jihar Bala Muhammad ya ce juriya, sadaukarwa, zaman lafiya, taimako da neman ilimi na cikin ababen da Manzon Allah ya koyar da sahabban sa masu daraja, don haka ne ya nemi al’umma da su yi koyi.
Gwamna Bala Muhammad ya bukaci Malamai da su daina sukar shugabanni a gaban dalibansu ba tare da kwararan hujjoji ba domin kyautata rayuwa a kowani lokaci.