Kamar yadda aka sani, fasaha ta rabu kashi daban-daban, kamar yadda kimiyya take, wato akwai wasu fannoni da aka samar a karkashinta sakamakon bunkasarta a zamanance.
Wadannan fannoni na fasaha sune suke gudanar da wannan zamani ta fuskar ci gaba. Sannan sun samo asali ne tun daga karnukan baya a tsohuwar duniya har zuwa yau.
Wadanda za a iya sani daga cikinsu sun hada da:
1. Communication Technology
Wannan fanni na fasaha da ake kira ‘Communication Technology’ shi ne fasahar sadarwa wanda tun a karnin baya ake amfani da shi. Misalan wannan fasaha sun hada da rediyo, da talabijin, da waya, da kuma yanar gizo. Wadannan fasahohin sadarwa da su muke amfani a kullum wajen isar da sakonni a fadin duniya.
2. Medical Technology
A fannin lafiya, sarrafa magani da likitanci, Medical Technology ya kawo muhimmin sauyi wajen zamanantar da duk wani sashe a fannonin. Kasashen da suka ci gaba suna amfani da wadannan fasahohi da aka samar don gudanar da gwaji, fida, sarrafa magunguna da sauran muhimman bangarori na harkokin lafiya da likitanci. Misali, kamfanin IBM ya kirkiri wani sakago da ke taimakawa likitoci wajen gudanar da fida.
3. Construction Technology
Duk wata gada, hanya, gini da makamantansu da ake gani yau sun danganta da fasahar gini da kira. Duk da ta kasance tun tala-tainin shekaru, amma an samu damar bunkasa ta, ta yadda a yau ta kasance mai matukar taimako ga kowa.
4. Information Technology
Fasahar bayanai kuwa ba karamin taimako na canji ta kawo ba a wannan duniyar. Duk wani lamari da ya shafi rumbun bayanai, na’ura, yanar gizo, fasahohin sadarwa duk sun ta’allaka ne a wannan rukuni kuma sune suka gina shi. Wannan fasaha ta zama ruwan dare a wannan zamani, don mafi yawancin manyan kamfanonin duniya a bangarenta suke. Misali kamfanin Google, Apple, Facebook da makamantansu.
5. Space Technology
Fasahar sararin samaniya ta taimaka matuka a yunkurin tafiya sararin samaniya. An hada da fannonin kimiyya da dama kamar bangaren Physics da Astronomy, da wasu fannonin fasaha don dace wa da abin da ake son ginawa. Ta dalilin wannan fasaha a yau ana iya kallon talabijin ta hanyar kirkirar tauraron Dan-Adam a ko ina a fadin duniya.
6. Artificial Intelligence
Fasahar fikira da ake kira Artificial Intelligence ta zama ruwan dare a wannan zamani duk da ba ta jima da kasantuwa ba. Wato fasaha ce da ake kokarin sanya wa na’ura, ta yadda na’urar za ta kasace mai basira da tunani da fikira kamar dan-Adam. A yau tasirin wannan fasaha ya yi sanadiyyar samar da babban ci gaba a fadin duniya, duk da ita ma tana da nata mukarraban.
7. Operational Technology
A yau, wannan fasaha kuma ita ta zama ruwan dare kusan fiye da sauran. Tana taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama. Misalanta sun hada da yadda ake kirkirar abubuwan zamani don saukaka wasu abubuwa da ake amfani da su, musamman wadanda suka kasance na gudanarwa a harkokin yau da kullum.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa